Bayan luguden wutan da Super Tucano ya yi wa mayakan ta’addanci da shugabannin ISWAP a Borno, sun yi taron kwana biyu a Borno inda suka sauya shugabanni.
Kamar yadda majiya mai karfi ta tabbatar, ‘yan ta’addan sun samu shugabancin Sani Shuwaram yayin taron inda kwamitin Shura da manyan kwamandoji suka bayyana Cikin yankunan da aka sauyawa kwamandoji akwai, Garal, Kayowa, Tumbum Murhu, Kurnawa, Chikun Gudu, Tumbumma, Kwalaram, Kirta, Wulgo da Jubuladam.
Kayi musharaka a wannan shirin na Patreon, mu hada kai wajen canza rayukan mutane! Borno – Bayan rashin manyan kwamandojin su da mayaka a luguden wutar da jiragen Super Tucano suka yi musu, shugabanni ISWAP sun yi sauye-sauyen mukamai.
PRNigeria ta ruwaito cewa, taron kwana biyun da suka yi tare da shugaban ISWAP, Sani Shuwaram, a cikin kwanakin karshen makon nan, ya samu halartar ‘yan kwamitin Shura da kuma kwamandojin yankunan Marte da suka hada da Garal, Kayowa, Tumbum Murhu, Kurnawa, Chikun Gudu, Tumbumma, Kwalaram, Kirta, Wulgo da Jubuladam da sauran sansanonin gagararrun kwamandojin ‘yan ta’adda.
Wasu daga cikin sabbin kwamandojin da aka nada sun hada da Abubakar Dan-Buduma wanda zai kula da yankin Bakassi Bunungil da Doron Buhari; Muhammad Ba’ana zai kula da yankin Kirta; Mohamet Aliamir zai kula da yankin Kwalaram; Bakura Gana zai kula da Jubularam; Malam Musa zai kula da Jubularam da kuma Mohamadu Mustapha zai kula da Marte. Kamar yadda majiyoyi suka sanar, a taron an tattauna rashin kwamandoji da mayakan da aka yi sakamakon luguden da jirgin Super Tucano na sojin saman Najeriya yayi.
Ya ragargagaji manyan ababen more rayuwarsu da suka hada da sansanin makamansu da kuma yankunan Marte da Abadam a Borno tare da wasu wurare na tafkin Chadi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Bayan wata da watanni ana rigingumu, Mai Mala Buni ya sasanta rikicin APC a Gombe A wani labari na daban, wani rahoton jaridar Daily Trust ya kawo cewa an harbe mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP da dama a arangamar da suke yi da dakarun sojojin Najeriya.
‘Yan ta’addan sun kai farmaki garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno a safiyar ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba. Wata majiya ta sanar da jaridar cewa mayakan ISWAP sun kai farmakin ne da misalin karfe 9:00 na safe.
Sai dai abun bakin ciki, an rasa wani Birgediya Janar da wasu jami’ai a yayin da suke kare kasarsu amma kuma rundunar sojin kasa da na sama suna ta tayar da ‘yan ta’addan ta hanyar yi masu ruwan bama-bamai.