Kungiyar malaman jami’o’in kasar nan (ASUU) sun yi zaman majalisar koli na NEC a kan batun yajin-aikinsu.
Rahotanni sun ce malaman jami’ar sun tsawaita wa’adin yajin aikin zuwa nan da makonni takwas Wani jami’in ASUU ya sanar da cewa ba za a dawo aiki ba a dalilin rashin cin ma matsaya da gwamnati.
Kungiyar ASUU ta malaman jami’o’in kasar nan ta yi zaman majalisar koli a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris 2022 a game da yajin-aikin da ta ke yi.
BBC Hausa ta fitar da rahoto a yau cewa malaman jami’a sun zabi su cigaba da wannan yajin-aiki na jan-kunne, hakan na nufin ba za a bude makarantu ba.
ASUU ta tsawaita yajin-aikin da ta ke yi da tsawon makonni takwas. Malaman jami’a sun ci ma wannan matsaya bayan wata guda ana zama da gwamnati.
Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau wanda ya zanta da BBC ya shaida cewa sun dauki wannan mataki ne domin ba gwamnati damar kai ga matsaya.
A cewar Farfesa Abdulkadir Danbazau wanda yana cikin ‘ya ‘yan kungiyar ASUU, watanni biyu sun isa dai gwamnatin tarayya ta yi duk abin da ya kamata.
Kamar yadda wani ‘dan jarida Alao Biodun ya bayyana a Twitter, a safiyar Litinin ake sauraron a ji matsayar da shugabannin na kungiyar ASUU suka dauka.
Hakan zai biyo bayan zaman majalisar koli ta NEC da malaman suka yi a jami’ar tarayya da ke Abuja da ke Gwagwalada. ASUU tayi zaman na NEC ne a jiya.
Biodun ya ce alamu su na nuna kungiyar ASUU ba za ta janye wannan yajin-aiki a yau ba. Dalili kuwa shi ne ba a tsaida magana da wakilan gwamnati ba.
Wani babban malami a jami’ar tarayya da ke garin Dutse, jihar Jigawa ya tabbatar da wannan mataki da kungiyar ASUU ta dauka a shafinsa na Facebook.
Da yake magana a dandalin, Dr. Aliyu Isa Aliyu ya ce an tsawaita yajin-aikin na malaman jami’a da makonni takwas. Za a fara lissafi ne daga 14 ga watan Maris.
Hakan na zuwa ne bayan kungiyar malaman jami’ar kasar sun yi wa hukumar NITDA raddi a kan UTAS, su ka ce har zuwa yanzu ana kan gwajin manhajar ne.
Ba mu da kudi – Gwamnati Kwanaki aka ji Ministan kwadago da ayyuka na tarayya, Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa ba su da kudin da ASUU ta ke nema domin a gyara jami’o’in kasar.
Chris Ngige ya fadawa manema labarai cewa a halin yanzu gwamnati ba ta da wadannan biliyoyin, sai dai idan za a yaudari malaman domin su koma aiki.