Bayan shafe kwanaki ana cece-kuce akan Janny Sikazwe, alkalin wasa dan kasar da ya jagoranci wasan da aka buga tsakanin Tunisia da Mali a ranar Laraba, an gano dalilinsa na busa usur din kawo karshen fafatawar kafin lokaci ya cika har sau biyu.
Sai dai a yayin da yake karin bayani akan lamarin, shugaban alkalan wasan da ke alkalanci a wasannin gasar cin kofin Afirka, Essam Abdel-Fatah, ya ce alkali Janny Sikazwe yayi fama ne da matsalar tsananin zafin da makinsa ya kai 34 a ma’aunin Celcius abinda ya haifar da karancin ruwa a jikinsa.
Abdel-Fatah ya kara da cewar ko bayan Karkare wasan da Mali ta doke Tunisia da 1-0 a filin was ana Limbe da ke Kamaru, sai da aka gaggauta garzawaya da Alkali Sikazwe asibiti domin ceto lafiyarsa.
A wani labarin na daban Takaddama ta barke tsakanin tawagar kwallon kafar kasar Burkina Faso da jami’an Kamaru, gabanin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka a kasar ta Kamaru, inda kaftin din Burkina Faso ya caccaki gwajin cutar Korona da aka yi musu.
Traoré da mataimakin kocin Burkina Faso Firmin Sanou sun ce tawagar likitoci sun taru a otal dinsu da ke Yaoundé da safiyar ranar Juma’a don gudanar da gwaje-gwaje, kuma lokacin da suka nemi tabbatar da shaidarsu, Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF, ta musanta aika tawagar jami’an lafiyar.
A halin yanzu dai sakamakon gwajin da tawagar likitocin suka fitar ya nuna cewar, kocin tawagar kwallon kafar Burkina Faso Kamou Malo da ‘yan wasan baya Sa’idou Simporé da Oula Abass Traoré da kuma dan wasan gaba Dango Outtara suna dauke da cutar Korona.