Mata da magoya bayan Sanata Albert Bassey Akpan, dan takarar gwamna na YPP, sun yi masa gangami a ranar Juma’a, 9 ga watan Disamba a karamar hukumar Etim Ekpo a jihar Akwa Ibom.
Babban kotun tarayya da ke Uyo ne yanke wa Sanata Akpan daurin shekaru 42 a gidan yari a ranar Alhamis Amma, matarsa, abokin takararsa da wasu magoya bayansa ba su dena masa kamfe ba.
Duk da cewa yana gidan yari, matar Sanata Albert Bassey Akpan, dan takarar gwamna na jam’iyyar Young Peoples Party, YPP, a jihar Akwa Ibom, sun fara kamfe a madadinsa.
The Cable ta rahoto cewa an yi kamfen din Akpan ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Disamba a karamar hukumar Ekpo karkashin jagorancin abokin takararsa, Asuquo Amba.
Legit.ng ta tattaro cewa daruruwan mutane ne suka halarci gangamin don nuna goyon bayansu ga sanatan da aka daure.
Akwa Ibom 2023: Matar Akpan ta yi magana Da ta ke jawabi ga magoya bayansa a wurin taron, Imabong ta ce babu gidan yarin da ke da girmar da zai iya dakatar da ‘abin da mutane ke so.’
Ta ce: “Sanata Bassey Albert -OBA har yanzu yana takarar, Zai ni nasara ba zai karaya ba.
Babu gidan yarin da ya isa ya dakatar da abin da mutane ke so.”
Shugaban kwamitin kamfe ya yi magana
A bangarensa, Emem Akpabio, shugaban kwamitin kamfen din, ya ce daure Sanata Akpan da aka yi ‘wani tsaiko ne na dan lokaci da aka yi don gwada imaninsu kuma a daukaka YPP zuwa matakin yanci.’
Ya kwatanta daure sanatan da tsohon shugaban kasa Nelson Mandela da Annabi Yusuf a Bible.