Wani dan Najeriya ya yada wani bidiyon lokacin da ya ciro damman Naira 5 daga banki ya rike a hannun sa.
A cewar mutumin, ya samo kudin ne daga wani bankin kasuwancin da yace bai samu manyan kudade ba.
‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar ciwon kai wajen nemo sabbin kudaden N200, N500 da N1000 da aka sauya kwanan nana.
Wani dan Najeriya ya bayyana kukansa na rasa manyan kudi a bankunan Najeriya, inda aka bashi wasu kananan kudade.
A cewar mutumin, an bashi ‘yan Naira 5 a banki kasancewar babu manya lokacin da ya je cire kudi a bankin kasuwanci.
A bidiyon da ya yada a TikTok ya nuna, mutumin ya bayyana kokensa kan yadda aka bashi ‘yan N5 a madadin manyan kudi.
Ba a dai san adadin kudin da ya cire ba, amma an ga dami takwas a hannunsa da suka cika fal.
Ya bayyana cewa, bankinsa ya bashi kudin ne alamar da ke nuna babu sabbin kudade ko wasu manya.
‘Yan Najeriya dai na ci gaba da fama da karancin sabbin N200, N500 da N1,000 a bankunan Najeriya.
Martanin jama’a a kafar sada zumunta @Egbe Adebukola: “Lallai ke mai arziki ce.”
@ARTHUR: “Rayuwa ta fara sauki yanzu kam.” @Ifeyinwa Eucharia Uyanneh: “Wannan ai horo ne.”
@hammed Aminat: “Ya kamata ka gode Allah ma ka ga N5 din har ka karba.”
@ADUNNI ADE: “Naira 5 a yanzu dai ya samu daraja, ba zan cire rai ba.”
@user9973819636447: “Malam kana bukata ne shi yasa ka karba to meye na korafi?”
@Ojuolape Oloyede: “A kalla dai kana da tsabar kudi a hannu.”
A halin da ake ciki, ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da yadda babban bankin CBN ya kawo batun sauyin kudi a shekarar nan.
A wani labarin, kun ji yadda wasu mazauna jihar Kebbi suka bayyana aniyar rufe kasuwancinsu saboda karancin sabbin kudade a kasar.
Wannan na zuwa bayan da gwamnatin Buhari ta ce za a daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 tare da maye gurbinsu da sabbi.
Babban abin da ake maida hankali a kai a Najeriya a yanzu shine yadda bankuna ke karancin sabbin kudaden.
Source:LegitHausa