Kotun shari’ar musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Murja Ibrahim Kunya, hukuncin sharar Asibitin Murtala na tsawon sati uku tare da zuwa Hisba tsawon watanni shida.
Aminu BBC da Ashiru Idris Mai Wushirya da Sadik Sharif za su yi sharar Masallacin Murtala har tsawon sati uku.
Tun da farko dai kotun ta tura Murja zuwa gidan yari na wucin gadi kafin yanke mata hukunci.
Wasu Malaman Shari’ar Musulunci a Kano sun shigar da kara kan Murja, inda suka zarge ta da bata tarbiyya a kafar TikTok.
An dai kama Murja ne a otal din Tahir da ke Kano yayin da ta ke kokarin gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarta a jihar.
Daga bisani aka sake kamo wasu daga cikin matasan da ke amfani da kafar ta TikTok, sannan aka tisa keyarsu zuwa gidan yari.
Wannan dai na daga cikin shirin masu ruwa da tsaki da ke jihar don ganin sun tsabtace kafofin sada zumunta.
A wani labarin na daban hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana Malam Ibrahim Shekarau na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Kano ta Tsakiya.
Wannan rudani ya biyo bayan lashe zaben Sanata da Rufai Hanga na jam’iyyar NNPP da ya yi a ranar Asabar.
Amma tun kafin shiga zaben, Sanata Shekarau ya bayyana cewar tuni ya fice daga jam’iyyar NNPP kuma ba shi da wata alaka da jam’iyyar.
Kuma ya ce ya aike wa da INEC a rubuce cewar ya fice daga jam’iyyar amma ta sanar da shi cewar lokacin sauya sunan dan takara ya wuce.
Ita ma a nata bangaren, jam’iyyar NNPP ta ce ta sanar da INEC sauya sunan Shekarau da na Rufai Hanga biyo bayan ficewarsa daga jam’iyyar tare da komawa PDP.
Amma ana tunanin NNPP na iya garzayawa kotun kararrakin zabe don kalubalantar ayyana Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben.