Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta lashi takobin lashe kofin gasar kasashen Afrika da za a fara gudanarwa daga ranar 9 ga wannan wata na Janairu a Kamaru zuwa 6 ga watan gobe na Fabairu.
Super Eagles ta Najeriya za ta yi wasanta na farko ne da Masar a rukunisu na D a ranar 11 ga watan nan, wasan da babu shakka zai dauki hankali matuka saboda zubin ‘yan wasan da kowanne bangare ke tunkaho da su.
Mohamed Salah na Liverpool ne zai jagoranci tawagar Masar wadda ta lashe kofin gasar Afrika har sau bakwai, yayin da Najeriya ta lashe sau uku, amma take fatan sake lashewa a karo na hudu.
Kodayake masana harkokin wasan sun fara hasashen yadda za ta kaya a fafatawar tsakanin kasashen biyu, inda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ke cewa, da yiwuwar Najeriya ta samu nasara kan Masar da ci 2-1.
Alkaluma sun nuna cewa, sau biyu kacal Masar ta doke Najeriya a daukacin wasannin da kasashen biyu suka yi a gasar ta cin kofin Afrika.
A wani labarin na daban Wasu mutane sun lalata mutum-mutumi na gwarzon dan wasan Argentina da ke taka leda a Barcelona Lionel Messi a birnin Buenos Aires, in da suka raba shi gida biyu.
A cikin watan Junin bara ne hukumomin kasar suka kafa mutum-mutumin bayan dan wasan ya gaza lashe gasar Copa America, abin da ya tilasta masa daukan matakin yin riyata daga buga wa kasarsa tamaula duk da dai daga bisani ya janye ritayar.
Hukumomin kasar sun ce, tuni aka fara gyaran mutum-mutumin wanda aka kera da tagulla.
Messi mai shekaru 29 na da magoya baya da ke nuna masa kauna a Argentina, sannan kuma akwai masu nuna masa akasin haka bayan sun zarge shi da rashin zage danse wajen buga wa kasarsa ta asali kwallon kafa kamar yadda ya ke nuna bajinta a Barcelona.