Jarumi Mato Yakubu, wanda yayi fice da sunan Malam Nata’ala Mai Sittin goma, ya nisanta kansa da bidiyonsa dake yawo na yabon Buhari.
Ya sanar da cewa, a baya shi ‘dan gani-kashenin shugaban kasan ne amma yanzu kuwa sun yi hannun riga da shi Yace rashin tsaro, matsin rayuwa da watsi da aka yi da su duka da kokarin da suka yi na kafa gwamnatin yasa ya dawo daga rakiyar Buhari.
Jarumin Kannywood wanda yayi fice a shiri mai dogon zango na Dadin Kowa, Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala mai sittin goma, ya barranta kansa da bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya inda aka gan shi yana yabon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A zantawar da yayi da Aminiya Daily Trust, Malam Nata’ala yace wannan bidiyon da ake yadawa tun 2015 yayi shi yayin da ake farkon mulki Buhari, amma a yanzu baya tare da shugaban kasan.
Jarumin masana’antar Kannywood in yace a baya shi masoyin shugaba Buhari ne kuma ‘dan jam’iyyar APC.
Malam Nata’ala mai sittin goma ya jaddada cewa, yayi bidiyon da yake kare Buhari amma hakan bai amfanar masa da komi ba.
Ya kara da cewa, wasu ne suka fito da bidiyon a halin yanzu suke yadawa don sun ga zabe na gaba na zuwa, suna son ci da guminsa ne.
“Zan fitar da sabon bidiyo domin barranta kaina daga tsohon bidiyon da nayi, kuma in sawarwara Allah ya isa ga duk wanda ya cigaba da yada shi,” cewar jarumin.
Ya bayyana cewa, dalilinsa na janye goyon bayansa daga shugaba Buhari shi ne matsin rayuwa da walaha da talakan kasar nan yake ciki yanzu.
Ya kara da bayyana trashin tsaro da sauran irin wahalhalun da kasar nan take ciki tare da watsi da aka yi da su bayan irin gudumawar da suka bada wurin kafa gwamnatin.
A wani labari na daban, jami’an ‘yan sanda a kasar Indiya sun cafke wasu mutane shida da suka dauka tsawon watannin takwas a matsayin ‘yan sandan bogi.
Ba a nan mutum shidan suka tsaya ba, sun bude caji ofis na bogi a wani otal inda suke karbe kudaden mutane hankali kwance, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.
Source: LEGITHAUSA