Wata mata ƴar Najeriya ta shiga damuwa bayan ta gano cewa mijinta magidanci ya yi wa mai koyon aiki a wajen ta ciki.
Matar auren wacce ta ke da wajen gyaran gashi, ko da yaushe tana tura mai koyon aiki a wajen ta zuwa gida domin ta yi mata aikace-aikace.
Abin takaici, sai ta fara kwantawa da mijin matar auren inda daga bisani ta samu juna biyu.
Wata matar aure mai gyaran gashi ta ga ta kanta bayan ta gano cewa mai koyon aiki a wajen ta tana ɗauke da juna biyu wanda mijinta ne ya ɗirka mata.
Matar auren tana tura mai koyon aikin a wajen ta zuwa gidan ta domin ta yi mata wanki da sauran ƴan aikace-aikacen cikin gida.
Magidanci ya ce mai koyon aiki wajen matarsa ta iya sarrafa shi.
Sai dai, a maimakon ta yi aikin da aka tura ta musamman domin ta yi, sai mai koyon aikin ta zaɓi ta zama makwafin mai koya mata aikin a wajen mijinta inda ta riƙa biya masa buƙatun sa.
Ta riƙa kwanciya da mijin matar duk lokacin da aka aike ta zuwa gidan har dai daga ƙarshe ta samu juna biyu.
Lokacin da matar auren ta gano abinda ya auku, sai ta lakaɗa mata dukan tsiya amma sai mijinta ya tsawatar mata inda ya bayyana yarinyar a matsayin ‘gishirin rayuwar sa’