Saudiyya ta bayyana cewa mutum 60,000 kacal ta amince du gudanar da aikin hajjin bana a faɗin duniya sakamakon cutar covid 19.
Ƙasar tace 15,000 daga ciki zasu fito ne daga ƙasar Saudiyya, yayin da 45,000 daga sauran ƙasashen duniya.
Saudiyya ta dakatar da gudanar da aikin hajji a bara sabida ɓarkewar cutar COVID 19 a duniya Ƙasar saudiyya ta bayyana adadin mahajjatan da zasu samu damar yin aikin hajji a wannan shekarar ta 1442 byan hijira, wacce tazo dai-dai da 2021.
‘National Hajj Commission Of Nigeria.’ Saudiyya tace adadin mutane 60,000 ne zasu samu izinin gudanar da aikin hajji a faɗin duniya baki ɗaya.
Hakanan hukumomin ƙasar sun fitar da dokoki dake ƙunshe da dukkan bayanan yadda aikin hajjin zai gudana. Idan baku manta ba Saudiyya ta dakatar da gudanar da aikin hajji ne sabida guje wa yaɗuwar cutar COVID 19.
Ana jin tsoron kada masarautar kasar ta saudiyya ta hana hajji bana dai amma a wani salo na ba sabun ba an ga kasar ta bari ayi aikin hajjin na bana amma a wani yanayi mai kama da da babu gamma ba dadi.
A wani labarin kuma Hukumar AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike Hukumar binciken haɗurra ta ƙasa AIB-N, ta bayyana cewa ta gano wani baƙin akwati na jirgin da yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojin Najeriya, Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10.
Hukumar tace ta gano FDR da CVR waɗanda ke naɗar bayanai da murya yayin da jirgi ke tafiya a sararin sama, ta kuma tabbatar da cewa zata gudanar da bincike mai tsanani.
Wasu dai suna zargin a kwai alamun an shirya kashe shugaban sojojin ne sakamakon wasu abubuwa dake tattare da hadarin jirgin na babban hafsan sojin kasan na najeriya General Attahiru.
Mahaifin direban jirgin ma yayi fatan Allah ya bayyana asalin dalilin mutuwar dan sa in d akalaman sa suke nuna alamun shakku dangane da silar hatsarin da kuma mutuwar dan nasa dam sauran fasinjojin dake cikin jirgin.