Sabon salon yajin aikin da ke guda a Jihar Kaduna bisa jagorancin kungiyar kwadago ta kasa (NLC) na ci gaba da daukan sabon salo, yayin da Gwamna Nasiru el-Rufa’i ya ayyana korar dukkan malaman asibiti da ke kula da majinyata wadanda suke kasa da mataki na 14 a tsarin aikin gwamnati.
Tuni gwamnatin jihar ta umarci ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar ta tallata neman sabbin malaman asibiti domin cike gurbin wadanda ta kora.
Sanarwar da ta fito daga mai taimaka wa gwamnan jihar a kan harkar yada labarai, Muyiwa Adekeye, ta ce Gwamna el-Rufai yana sake sabon gargadin cewa duk wani ma’aikacin da ba a gan shi a bakin aiki ba za a kore shi.
Sanarwar ta ce ta lura likitoci da wasu ma’aikatan kiwon lafiya suna kokarin aiki a asibitoci amma wasu malaman asibiti sun shiga sabon yajin aikin domin yin zagon kasa ga sha’anin kiwon lafiyar jihar. Ta zargi wasu malaman da sallamar marasa lafiya ta karfi da yaji a wasu asibitoci.
“Rahotanni daga Asibitin Koyarwa na Barau Dikko sun bayyana cewa wasu malaman asibiti uku da aka gano su, sun katse numfashin da wata jaririya ‘yar kwana biyu ke shaka ta bututu a ranar Litinin 17 ga Mayun 2021. An tura sunayen wadannan malaman asibitin zuwa ma’aikatar shari’a domin gurfanar da su a gaban kotu matukar wannan jaririyar ta mutu.
“Ma’aikatar kiwon lafiya za ta sallami dukkan malaman asibiti ‘yan kasa da mataki 14 da suka shiga yajin aikin da ya saba wa doka. Albashinsu za a bai wa abokan aikinsu da suka zo aiki don cike gurbinsu a matsayin alawus na musamman.” In ji sanarwar.
A wani bangaren kuma, gwamnatin jihar ta Kaduna ta fara harar malaman makarantu da suka shiga yajin aikin, inda sanarwar gwamnatin ta ce “Duk wani ma’aikacin Jami’ar KASU da ya ki zuwa aiki za a kore shi. Mahukuntan jami’ar za su mika kwafin kundin rajistar zuwa aiki na kullum na kowane matakin ma’aikata ga sakataren gwamnatin jiha da kuma kwamishinan ilimi. Haka nan sauran ma’aikatu za su mika kundin rajistar ga ofishin shugaban ma’aikata na jihar.
el-Rufai Ya Bazama Neman Shugaban Kungiyar Kwadago Ido-rufe
Gwamna Nasir el-Rufai ya ayyana neman shugaban kungiyar kwadagon Nijeriya (NLC), Kwamared Ayuba Wabba da sauran mambobin kungiyar ido-rufe.
An ayyana neman su ido-rufen ne a kan zargin yin zagon kasa ga tattalin arziki da kai hare-hare kan kayayyakin gwamnati kamar yadda yake kunshe a karkashin dokar aikata laifuka.
Gwamna el-Rufai, a cikin wani shafinsa na manhajar Tweeter a ranar Talata, ya ce, “an ayyana neman Ayuba Wabba da wasu ‘yan kungiyar kwadigo don lalata tattalin arziki da hare-hare a kan kayayyakin Gwamnati a karkashin dokar aikata laifuka.”
Ya ce, “duk wanda ya san inda yake boye ya aika sako zuwa @MOJKaduna KDSG. Za a sami kyauta mai tsoka”
A wani sakon Tweeter, ya ce, “duk wasu abubuwan ci gaba a jihar sun tsayar da shi cik. Ba za mu ja da baya ba ko kuma yarda da duk wata kutse da lalata ta siyasa.”
A baya an ruwaito Gwamnatin jihar tana cewa, yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da kungiyar kwadago ta NLC ta fara, wanda ya fara a ranar Litinin, ba zai dauke hankalin ta daga shirinta na kwato wa ma’aikatan gwamnati hakki ba.
Amma Wabba, wanda ya yi jawabi ga ma’aikatan gwamnati a jihar a ranar Litinin, ya sha alwashin durkusar da gwamnatin el-Rufai har sai an mayar da korarrun ma’aikata wajen ayyukansu.
Ina Nan, Ka Zo Ka Kama Ni – Kwamared Wabba
A halin da ake ciki kuma, Shugaban NLC na kasa, Kwamared Ayuba Wabba ya mayar da martani na ayyana neman sa ruwa a jallo da Gwamna el-Rufai ya yi, a ranar Talata, inda ya ce yana nan babu inda ya je, gwamnan ya zo ya kama shi.
Ayuba Wabba ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci ma’aikatan da ke yajin aikin zuwa fadar gwamnatin jihar a ranar Talata domin yin zanga-zanga, inda ya nunar da cewa idan gwamnan ya isa ya zo ya kama shi.
“Ya zo ya kama ni din. Muna nan a nan muna jiran su,” kamar yadda Jaridar Dailytrust ta ruwaito shi yana fada.
Kasuwar Wuraren Shakatawa Ta Bude A Kaduna
Kasuwa ta bude wa wuraren shakatawa da holewa a Kaduna domin kuwa wadanda suka mallaki wuraren suna kara samun wadanda ke zuwa harka, duk kuwa da yake ana cikin yajin aikin da kungiyar kwadago ta kasa raeshen Jihar Kaduna ta kira.
Manema labarai wadanda suka zagaya domin ganwa idanun su abubuwan da suke faruwa, sun bayyana cewa yanzu wuraren shakatawa suna budewa ne da wuri, ba kamar a kwanakin baya da suke fara yin harkokin nasu da yamma.
Mrs Cordelia Benedict, wadda tana da wurin da ake dan shakatawa a Gwari Abenue, ta bayyanawa manema labarai cewar ranar Talata, ta samu karuwar masu zuwa ne tun daga ranar Litinin lokacin da aka fara shi yajin aikin.
Ta yi karain bayani inda ta ce” Mun fara samun karuwar masu zuwa tun daga ranar Litinin lokacin da aka fara yajin aiki, harkar tamu tana tafiya.
“Yawancin mutane suna zuwa nan ne domin su yi cajin wayoyin su, ya yin da suke hutawa suna kallon wasan kwallo a, akwatuna talbijin namu.
“Maganar gaskiya ribar mu karuwa take yi a kwana dayan daya wuce, domin mutane suna fara zuwa nan ne tun daga karfe goma na safe kamar yadda ta bayyana.”
Shi kuwa mista bictor Iheme, wanda shi ma yana da wani sanannen wurin da ake hutawa wanda yake kusa da kwanar zuwa NNPC, ya bayyana dalilin hakan ne nasamun karuwar mutane kan wasu basuyb son su zauna gida ne domin akwai damuwa.
“Wasu daga cikin abokan ciniki na sunna yin ayyuka ne a ofisoshi, ko kuma abokai wadanda suke zama kusa da nan, kuma tun da yake an fara shi yajin aikin, mutane suna fitowa da wuri domin su shakata kamar dai yadda ya bayyana”.
Iheme ya ce rashin wutar lantarki ya sa mutane suna barin gidajensu da safe domin kawai su shakata.
“Wasu daga cikin abokan cinikinmu sun zo nan ne cajin wayarsu, ga ma wayoyin nasu da suke cazawa nan, hakanan ma suna sayen kayan sha.
“Duk da yake dai muna ka kudi wajen sayen man fetur domin shi janareto ya kasance yana cikin aiki, amma ribar da muke samu abin da akwai jin dadi da murna.”
Ita kuma Mrs Abigail Patrick wadda take gasa kifi akan kwanar Halima ita ma ta bayyanawa manema labarai cewar tana samun karuwar masu saye, inda kuma ta kara da cewa “Ina sanar da fiye da Kifi 30 na Tarwada ranar Litinin, wanda a kwanakin baya abin ba haka yake ba, musamman ma ace da safe ne.”
Manema labarai sun bada rahoton cewa reshen Jihar Kaduna na kungiyar kwadago ta kasa, ranar Litinin 17 ga watan Mayu 2021 ta fara yajin aiki wanda yake na gargadi ne ko kuma jan kunne na kwana biyar, dangane da wasu ma’aikatan daga kora aiki a Jihar.
Gwamna el-Rufai Ya Sallami Ma’aikata 60,000 A Shekara 6, In Ji Falana
Babban Lauya na kasa, Femi Falana da kungiyar ASCAB sun bayyana cewa a cikin shekara shida na mulkin Malam Nasiru el-Rufai, an kori ma’aikata kusan 60,000 a jihar Kaduna.
Wanda kididdiga ke nuna cewa Gwamna Nasir el-Rufai yana korar ma’aikata 280 ke nan a kullum.
Femi Falana, a wata ganawa da ya yi da manema labarai ya yi zargin cewa korar Ma’aikatan da ake yi ne ya jawo matsalar rashin tsaro.
Fitaccen Lauya mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana da kungiyar ta ASCAB sun soki gwamnatin jihar Kadunan da sabon rashin tausayi.
Femi Falana da kungiyar ASCAB sun bayyana cewa, Gwamna Nasir el-Rufai ya sallami ma’aikata 60,000 tun bayan da ya karbi mulkin Kaduna a Mayun 2015.
Binciken Femi Falana SAN sun nuna goyon bayansu a kan yajin-aikin da kungiyoyin kwadago su ka soma a Kaduna.
A wani jawabi da kungiyar ASCAB ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga duk wadanda suke karkashin kungiyar kwadago ta NLC su shiga wannan yajin-aikin.
ASCAB ta ce, sai an yi da gaske domin ayi maganin sallamar tulin ma’aikata da talauci da sabon rashin tsaron da aka jefa al’ummar jihar Kaduna a gwamnatin APC.
Femi Falana ya ce, tun fil azal, ma’aikatan gwamnati da na masaku ne suka rike tattalin arzikin Kaduna. Jaridar Punch ce, ta fitar da wannan sabon rahoto a ranar Litinin.
Falana yake cewa a shekarun bayan nan ne duk wadannan matatu suka mutu, aka kori ma’aikata daga aiki da-dama ba tare da an biya su wasu hakkokin sallama ba.
Lauyan ya ce, a maimakon Gwamna Nasir El-Rufai ya yi maganin wannan matsala, sai ya kori ma’aikata kusan 60,000, sannan aka hana mafi yawansu hakkin su.
“Jihar Kaduna ta na da hadarin zama ko aiki a Nijeriya, a dalilin yawan kashe-kashe, garkuwa da mutane, zubar da jini, rikicin kabilanci da addini,” In ji Falana SAN.
Har ila yau, Lauyan ya ce, ana fama da matsalar tsaro ne saboda yawan korar mutane daga aiki da gwamnati ta ke yi, ya ce, keta hakkin ma’aikata ne ya haddasa hakan.
Lauyan ya kara da cewa, an kori ma’aikata 13,000 a 2016, sannan aka sallami wasu 40,000 a 2017. Daga nan aka fatattaki malamai 21,000 a bana kuma an kori ma’aikata 17,000.
Kawo yanzu akwai sabon shirin na korar ma’aikata 11,000 daga aiki, a cewar Falana.