Jaruman fim suna daukar lokaci tare lokatan shirya fim, wanda hakan ke jawo abota ko kulluwar zazzafar soyayya.
Baya ga fitowa a matsayin ma’aurata ko masoya a fim, da yawan jaruman kan yi soyayya a zahiri, kamar yadda ake gani a fina-fiJaruwamnnan.
A Kannywood, masana’antar fina-finan Hausa a Arewacin Najeriya, akwai labaran jarumai da suka fada soyayya da abokan aikinsu da dama.
Wasu akan kai ga aure, amma wasu suna katsewa kafin a kai matakin.
Daily Trust ta zaklo wasu daga cikin jaruman Kannywood da suka yi soyayya amma ta lalace daga baya.
Fatima Abdullahi, da ta fi shahara da Fati Washa, na daya daga cikin jarumai mafiya sanuwa a Kannywood.
Haifaffiyar Bauchi ce, ta fara fim kusan shekara 10 da su ka wuce, ta yi fina finai sanannu kamar Yar Tasha, Hisab, Farida da kuma shirin Labarina mai dogon zango.
Jarumar mai shekara 30 ta taba soyayya da daya daga cikin manyan jaruman masana’antar, Adam A. Zango, jarumi kuma mai shirya fim, cike da zazzafar soyayya da ta kusa kaiwa ga aure.
Rahoto ya bayyana sun bata bayan shafe shekara hudu ana soyayya.
Tun bayan nan, Zango ya yi aure tare da sakin wasu mata biyu daban, amma ba a sake jin labarin soyayyar Washa ba.
Nafisa Abdullahi Adam A Zango da Nafisa Abdullahi.
Nafisa ita ma babbar jaruma ce wadda ake matukar rububi a Kannywood.
Haifaffiyar Jos din ta lashe lambobin yabo da dama, ta kuma yi fina-finan Nollywood.
Bayan sun yi fina-finai da dama da abokin sana’arta, Adam A. Zango, ko dai a matsayin masoya ko ma’aurata, zafafan hotunan jaruman ya cika shafukan sada zumunta don nuna irin alaka mai karfi da ke tsakanin jaruman, kafin daga bisani a fahimci soyayya su ke.
Daga baya Zango ya bayyana cewa sun shafe shekara uku su na soyayya kuma ya na da niyyar aurenta kafin kaddara ta gifta, wanda ke nufin an rabu.
Ya ce: “na so Nafisa sosai kuma mun kusa yin aure kafin mu rabu.” Fati Muhammad Fati Muhammad da Ali Nuhu.
Fatima Muhammad tsohuwar jaruma ce da ke cikin mafiya dadewar jarumai mata a Kannywood, ta shafe sama da shekara 20 a masana’antar.
Ta yi fitattun fina-finai kamar Sangaya, Zarge da Marainiya, kafin ta auri jarumin fim, Sani Musa Mai-Iska, ta kuma koma birnin London, duk da auren ya mutu bayan wasu shekaru.
Sai dai, alakarta da babban jarumi, Ali Nuhu, ya sanya masoyanta na ganin cewa jarumi Ali Nuhu ya so aurenta kafin da hadu da Sani Musa Mai Iska ta aure shi.
Da ta ke sharhin maganar, ta ce tabbas suna da alaka mai kyau da Ali Nuhu, kuma sun taba soyayya da Ali Nuhu amma ba su shirya yin aure ba.
“Ka san aure da mutuwa abu ne a hannun Allah, duk da alaka ta da Ali Nuhu, na auri wani daban. Amma duk da haka Ali dan uwa ne a wajena.” ta fada a wata hira.