Sakamkaon tambayoyi da ake ta samu daga mutane daban daban inda suke tambayar dalilin da yasa mabiya sheikh ibrahim zakzaky na najeriya wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a suke shirya tattaki duk shekara, duba da hakan yasa muka kawo muku wasu kadan daga cikin dalilan da yasa mabiya malam zakzaky suke gudanar da wannan ibada ta tattaki duk shekara.
Da farko dai ya kamata a sani cewa shi tattaki asali anayin sa ne a kasar iraki domin can ne garin karbala yake wanda asali karbala daji ne, a wannan daji shekaru dubu daya da kusan dari uku da suka gabata aka kashe daya daga cikin jikokin manzon Allah (S.a) tare da iyalan sa da kuma sahabban sa.
Tarihi ya tabbatar da cewa bayan an kashe Imam hussain (S.a) tare da wasu sahabban sa, sauran wadanda suka saura na daga iyalan gidan sa wadanda suka hada da mata da kananan yara an jasu a kasa tun daga karbala har zuwa dumaishq, wanda yanzu haka tana cikin kasar siriya ta yanzu.
An ja iyalan gidan annabta tun daga karbala ta kasar iraki har zuwa dumaishq ta kasar siriya, bayan ‘yan kwanaki kuma aka dawo dasu suka kuma bi ta karbalan dai a hanyar su da komawa madina bayan sarkin lokacin yazidu (L.a) ya bada umarnin a maida su madinan.
Tarihi ya tabbatar da cewa tun daga wannan lokaci ake samun masoya Imam hussain (S.a) suna tattakawa daga garuruwan su domin zuwa karbala su ziyarci Imam hussain (S.a), kuma Alhamdulillah a yanzu wannan taron tattaki wanda ake yi a kasar iraki shine taron da yafi kowanne taro tara jama’a
Wani yana iya tambaya yace, tom tunda a iraki akayi komi kuma yanzu ma a iraki akeyin tattaki tom mene kuma akeyi a najeriya?
Amsa itace wasu daga cikin masoya Imam hussain (S.a) wadanda suke a najeriya kuma basu da damar zuwa iraki domin yin musharaka a wannan babbar ibada sakamakon matsin tattalin arziki da sauran matsaloli sai suka ga dacewar samar da wani yanayi mai kama da wancan a nan gida najeriya domin a kalla massala wannnan babbar ibada, amma ba ance wanda baiyi musharaka yana da wani laifi bane a’a wanda dai ya ga yana da sha’awa shine yake shiga ayi dashi.