Wani barasarake a jihar osun, Olowu Of Owu-Kuta, Makama Oyelude ya bukaci mai rajin kafa kasar yarabawan nan sunday ayemo wanda aka fi sani da sunday igoho da ya ajiye fafutukar sa ta kokarin kafa kasar yarabawa kuma ya gaggauta mika kansab ga hukuma domin kawo karshen rikita rikitar da ke faruwa a yankin na yarabawa.
Shi dai sunday igoho jami;’an tsaron najeriya sun jima da baza komar neman sa inda suka bukaci da yaggaguta mika kansa ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin samawa kansa sauki.
Jami’an tsaron sun bukaci sunday igoho ya mika kansa ne bayan sun kai wani samame inda suka kashe daya daga cikin na tare da sunday igoho din, yayin da unday igoho ya samu tserewa kuma aka nemi inda yake aka rasa zuwa yanzu.
Loakacin da yake amsa tambayoyin manema labarai basaraken na bangaren yarabawa ya bukaci sunday igoho ya mutunta dokokin kasa domin samun zaman lafiya inda ya kamata kokarin na sunday igoho na kafa kasar yarabawa a matsayin wani kuskure kuma wanda bazai yi wani tasiri ba saboda haka ajiye wannan batu shine abinda zaifi zama mai amfani ga sunday igoho dama al’ummar yarabawa gabadaya.
Mataimakin shugaban kasar najeriya mai ci ya fito ne daga bangaren yarabawa kuma yarabawa sunyi mulkin najeriya na shekaru baya bayan nan shine lokacin shugaba olusegun obasanjo wanda ya shafe shekaru takwas yana mulkin najeriya bayan wancan zangon da yayi, abinda mutane ke tambaya shine menene dalilin da wasu daga cikin yarabawa zasu nemi ballewa daga najeriya bayan a kalla ana damawa dasu a cikin lamuran gudanarawa da lamurran mulki a kasar ta najeriya sbanin ibo da suke ganin kamar an ware su ne ko kuma an maida su saniyar ware ne a sabgogin gudanarwa da mulki a tarayyar najeriyar.
A na iya cewa taraayyar najeriya dai bata taba samun wani kalubalen neman ballewa daga najeriya irin na wannan karon ba .