A ganawar da babban malamin mazhabar shi’a na afirka ya yayi da manyan almajiran sa a babban birnin tarayyar abuja, sheikh zakzaky ya bayyana kisan kiyashin zariya na shkara ta 2015 a matsayin jarabawa da al’ummar najeriya gabadaya wanda hakan yake nuna a kwai bukatar kowa ya wanke zuciya kuma aji tsoron Allah ta’ala.
Sheikh Ibrahim zakzaky wanda ya samu ‘yancin kansa bayan tsare shi da gwamnatin tarayya gami da gwamnatin jihar kaduna tayi na tsawon shekara shidda ya bayyana cewa sharri baya samun mumini saboda haka wannan lamari ba komi ya kara masa ba sai tsoron Allah ta’ala da kuma kara mika lamurran sa ga Allah madaukakin sarki.
Sheikh zakzay ya bayyana cewa wadanda suke da hannu a aiwatar da kisan kiyashin zariya basu iya cimma muradan su wadanda suka ingiza su ga aikata wannan mummunan aiki ba, kuma tun daga wanna lokaci lamurran su suka soma dagulewa kuma har zuwa yau basu samu yadda suke so ba saboda haka ya musu nasiha da cewa ya kamata su ji tsoron Allah su nemi gafarar Allah ta’ala da kuma wadanda suka zalunta a wannan lamari.
Daya juya bangaren Almajiran sa shehin malamin ya tabbatar musu da cewa wannan jarabawa dai an cinye ta amma kamar yadda kowa ya sani gabadayab rayuwa jarabawa cea saboda haka kowa ya shirya ma wata sabuwar jarabawar saboda haka a kwai bukatar a sabunta niyya kuma a hada kai domin yin aiki tare.
A shekarar 2015 ne dai sojoji bisa jagorancin babban hafsan sojin najeriya na mwancan lokacin janaral tukur byratai suka kaima malamin hari gami da kashe da dama daga cikin almajiran sa ciki har da ‘ya’yan sa ukku maza.
Tun wancan lokacin dai ake tsare da malam zakzaky sai ranar 28 ga watan yuli ne kotu ta sani malamin kuma ta bada umarnin a sake shi ba tare da sharadi ko sake kama shi ba.
Masu lura da lamurra sun tabbatar da cewa shehin malamin ya nuna dattako domin a tsawon shekaru shidda da yayi yana hannun hukuma bai taba yadda almajiran sa sunyi wani abu mai kama da tashin hankali ba.