Sheikh Ahmad Magmud Gumi yana cikin manyan malamai wadanda muryar su take amsa kuwwa a tsakanin malaman najeriya kuma yana cikin malamai wadanda suka shahara a bangaren wahabiyawa.
Sheikh Gumi dane ga tsohon babban malamin nan wanda ake zargin shine ya kawo aklidar wahabiyanci najeriya watau, Mahmud Gumi wanda kuma shine wanda ya kirkiri kungiyar wahabiyawan nan ta izalatul bid’ah wa iqamatussunnah wacce ta shahara da IZALA a takaice.
Kwanan baya bayan nan mun jiyo duriyar sheikh gumi yana ta kokarin samar da zaman lafiya a yankin arewacin kasar nan, malam gumi ya bayyana shirin sa na aiki tare da jami’an tsaro domin samar tsaro ami da zaman lafiya a arewacin najeriya.
Tun dai shekarun baya da suka wuce aka rasa zaman lafiya wwanda hakan ya zama babbar barazana ga rayuwar al’umma kuma gwamnatin najeriyar ta kasa magance wannan babbar matsala data addabi al’umma.
Wakilin mu ya bibiyi lamarin inda ya tattaro mana bayanai dangane da yiwuwar samun mafitar tsaro ta hanyar sheikh ahmad gumi.
Da farko malam gumi bawahabiye ne kuma yana bin takarkin da manyan kungiyoyin ta’addanci na duniya irin su ISIS, Boko haram, taliban da sauran su.
”Idan gwamnati ta bama malam gumi dama domin samar da tsaro a arewacin najeriya, babu abinda zai karu illah rashin tsaro” kamar yadda wani mazaunin arewacin najeriya ya tabbatar mana.
An tabbatar da wasu da yawa daga cikin masu garkuwa da mutane dake a daji sun zama wahabiyawa kuma ana zargin tasirin shigar shehin malamin dazukan ne ya tabbatar da samuwar hakan.
Al’ummar arewacin najeriya suna cikin halin tsoro gami da dar dar dangane da tsomala bakin sheikh gumi a lamurran tsaron arewacin najeriya kuma da yawa sunyi kira da cewa lallai kada gwamnati ta bama malam gumi kowacce irin dama a wannan bangaren duba da cewa kasar saudiyya ma ta sanya cikin jerin wadanda take zargi da ayyukan ta’addanci.