Sabuwar cutar wacce akayi ma take da ”Delta” kuma masana suna tabbatar tafi ainihin cutar ”covid 19” karfi gami da saurin yaduwa ta fara mamaye manyan garuruwan amurka ciki har da babbar birnin kasar watau New York.
Masan sun tabbatar da cewa sabuwar cutar korona biros din ta ”delta” tafi koronar in gila da ta indiya dama ta afrika ta kudu illah.
Kasashen duniya da dama dai ciki har da jamhuriyyar msulunci ta Iran sun dauki matakin rigakafi domin tabbatar da cuwa sabuwar cutar wacce ta bulla a amuirka bata isa kasashen su ba.
Hukumar lafiya ta duniya ta gargadi mutanen duniya dangane da bullar sabuwar cutar inda ta bukaci mahukuntan kasashen duniya da su dauki matakan kare ‘yan kasshen su wanda hakan ya hada da kula da dokokin kiyaye lafiya gami da kokarin rage yawan cunkoso da tafiye tafiye gami da kula da baki ‘yan kasashen waje masu shigowa inda aka tabbatar itace babbar hanyar da cutar tafi amfani da ita wajen shiga kasar da babu ita.
Hukumomi a kasar amurka sun sha alwashin ganin bayan cutar ta korona biros wacce ta bayyana mai sun adelta amma sai dai tun ba’a je ko’ina ba gazawar su ta bayyana afili sakamakon yadda cutar ta kusa mamaye kowanne bangane na kasar ta amurka.
A wani labarin na daban kafar yada labaran nan ta The Cable ta rawaito shugaban kasa buhari yana bayyana cewa sabuwar hanyar da gwamnatin sa ta kirkiro na inganta ayyukan noma kwalliya ta biya kudin sabulu.
Shugaba muhammadu buhari ya tabbatar da cewa nasarar da sabuwar hanyar ta samu ne ya sanya da yawa daga cikin manyan ma’aikatan gwamnati ke barin ofisoshi suna komawa gona domin cin gajiyar sabuwar hanyar noma da gwamnatin ta samu nasarar kirkirowa.
Sai dai da dama daga cikin ‘yan najeriya yayin tofa albarkacin bakin su sun bayyana ikirarin shugaban kasar a matsayin wanda bashi da tushe balle makama domin ba’a taba shiga halin matsi da yunwa irin na lokacin shugaba buharin ba a tarihin kasar ta tarayyar najeriya.