Biyo bayan takardar neman ajje aiki na tsohon alkalin alkalai kuma sabon shugaban kasar Iran ya shigar gaban jagoran juyin juya halin musulunci na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda hakan ya biyo bayan kokarin sa na shirya sabuwar gwamnatin sa wacce zata soma aiki nan ‘yan kwanaki.
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali-Khamene’i ya nada hujjatul islam muhsini ijehiy a matsayin sabon alkalin alkalan kasar ta Iran kuma wanda zai gaji Ayatullah Ibrahim Ra’esi wanda yanzu yake zaman sabon zababben shugaban kasar ta Iran.
Dama dai kamar yadda kundin tsarin mulki na Iran din ya tanadar jagoran shine ke da alhakin nada alkalin alkalan kasar a duk lokacin da bisa kowanne irin dalili kujerar ta alkalin al;kalai ta zama babu kowa.
Ana sa ran a samu hadin kai tare da aiki tare tsakanin bangaren shari’a dana zartarwa a wannan lokacin domin dama sabon shugabn kasar sayyid Ibraheem Ra’esi da kuma sabon alkalin alkalan hujjatul islam muhsini abokan aiki ne a ma’aikatar shari’a tun shekaru kusan talatin da suka gabata wanda ake sa ran hakan zaiyi babban tasiri wajen fahimtar juna gami da aiki tare tsakanin bangarorin biyu.
Tuni dai kafar sadarwa mallakin jamhuriyar muslunci ta Iran din mai suna Tasnin ta sanar da sabon nadin kuma tuni mutane daga ciki da wajen kasar ta Iran suka fara aikawa ta sakonnin taya murna gami da Allah rika ga sabon shugaban bangaren shari’a kuma alkalin alkalai na kasar.
Jamahuriyar musulunci ta Iran na cikin kasashen dake fama da takunkuman tattalin arziki wanda kasar amurka ta kakaba mata sakamakon bambancin manufofin siyasa.
Masana siyasa da tattalin arzikin duniya sun tabbatar da cewa jamhuriyar musulunci ta Iran ta iya shallake shingayen takunkuman tattalin arizkin da amurkan ta kakaba mata ba tare da sun haifar mata da wata gagarumar matsala ba wanda hakan ya bata damar zama daya daga cikin manyan kasashe masu karfin fada ajia aduniya bbaki daya.