Kotu a jihar kadunan najeriya ta saurari lauyoyin malam zakaky dana matar sa malama zinatuddin kamar yadda ta saurari lauyan gwamnati kuma ta sanya ranar ashirin da takwas ga watan yulin nan da muke ciki na shekarar 2021 domin yanke hukuncin karshe bisa bukatar da lauyan malamin Brrister Femi Falana SAN ya shigar na ”NO CASE SUBMISSION” Ma’ana dai kotu tayi watsi da karar da gwamnatin kaduna ta shigar domin bata da tushe ballantana makama kamar yadda shaidu suka tabbatar.
Alkalin kotun wanda ya samu halartar kotun a safiyar ya saurari wata shari’a kafin ya kira shari’ar da aka shigar da shaihin malamin, bayan karasowar babban lauya falana an soma gabatar da shari’ar inda Barrister femi falana SAN ya tabbatarwa da kotu cewa duk shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar sun gaza alakanta wanda ake tuhuma da laifukan da aka ayyana, dadi a kan hakan kuma wannan kotun tayi shari’ar wadanda aka zarga da aikata laifukan da akace ana zargin malamin addinin da taimakawa aiwatar dasu, inda mista falana ya tabbatar da cewa tunda asalin wadanda ake tukuma da aikata laifi kotu ta wanke su kuma ta sallame su, to babu dalilin rike wanda ake tuhuma da taimakawa wajen aikata wannan laifin.
Lauyan mai dakin malamin ma ya bayyana cewa duk shaidun da aka gabatar ko sunan wacce yake karewa basu iya sun ambata saboda haka ya kamat kotu ta yanke hukunci yadda ya kamata ma’ana ta sallami wacce yake karewa.
Daga baya lauyan gwamnati bayero dari yayi bayanan kare kai inda yake kotu tana iya sakin wanda ake tuhuma da laifi kuma ta hukunta wanda ake tuguma da taimakawa wajen aikata wannan laifin, wanda wannan bayanin ya bama kowa dariya a kotun ciki har da Barrister Femi Falana SAN wanda yace yana ma dari fatan ya zama SAN somin kara samun gogewa a bangaren shari’a.
An tashi a kotu a yau amma ana sa ran ranar 28 ga watan july 2021 kotun zata wanke wadanda ake tuhuma kamar yadda yake a ka’ida