Jagoran wanda ya bayyana haka a ganin sa na karshe da gwamnatin shugaba hassan rohani wacce ta share tsahon shekara takwas tana gudanar da lamurran mulki na jamhuriyar musulunci ta Iran.
Jagoran ya tabbatar da cewa a kwai babban darasi wanda ya zama wajibi sabuwar gwamnatin shugaba sayyid Ibraheeem ra’esi wacce zata kama aiki a kwanaki masu zuwa ta dauka.
Babban darasin shine gujewa yarda da amurka da kasashen yammacin turai a dukkan sabgogin gudanarwa na jamhuriyar musulunci ta Iran din.
Kamar yadda jagora Sayyid Ali Khamen’i ya tabbatar cewa, duk bangarorin da gwamnatin hassan rohani ta mika yardar ta ga amurka da kasashen yamma bata ci nasara ba amma duk bangarorin da ta dogara da kanta bata biya ta yaudarar amurkan da kasashen yamma ba tacin nasara.
A cewan jagoran wannan babban darasi ne wanda gwamnati mai kamata ya kamata ta lura dashi sosai domin kada ta maimaita kusakusan da gwamnati mai shudewa ta aikata.
Kasar jamhuriyyar musulunci ta Iran dai na zaman kasar da tafi kowacce kasa a fadin duniya fama da takunkumai wadanda suka hada dan atattalin arziki da sauran su.
Wakilin mu na bangaren labaran duniya ya tabbatar mana da cewa kusan kowanne bangare na gudanarwar jamhuriyar musuluncin ta Iran din sai da amurkan ta kakaba masa takunkumi, lamarin da hatta bangaren ilimi da al’adu bai tsira ba takunkuman na amurka musamman a lokaci shugaban amurka donald trump.
Ranar talata mai zuwa ne dai wanda yayi dai dai da 3 ga watan augusta ake sa ran sabuwar gwamnatin shugaba Ibrahim Raesi zata karbi ragamar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran din.
Fatan da iaraniyawa suke dashi dai shine, sabuwar gwamnatin da suka zaba a kwanakin baya zata lura da bayanai gami da jan hankalin jagora sayyid Ali Khamene’e domin sunhyi iman i da cewa da hakan ne kawai za’a samu cigaba dawwamamme a kasar mai karfin soji da tattalin arziki kuma mai karfin fada aji a gabas ta tsakiya.