Harin wanda kungiyar neman ‘yancin al’ummar Iraqi, wacce kuma ‘yan asalin kasar ta iraki ke gudanarwa ya zo ma amurka da isra’ilan bisa yanayin da ake kira da bazata domin ya raunata da dama daga cikin manyan jami’an sojin su a yayin da wasu daga cikin manyan jami’an na soji suka rasa rayukan su a sanadin harin wanda aka bayyana shi a matsayin na daukar fansa sakamakon harin ba sani ba sabon da sojojin amurka suka kai kan ‘yan kungiyar ta neman ‘yancin Iraki a satin daya gabata.
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar ”Fleet master chief james” wanda babba ne a ma’aikatan sojin amurka tare da wasu manyan sojoji guda hudu suna cikin wadanda harin ya rutsa dasu.
Laftanal kanal james c. wlliams, da kanal sharon Asman na cikin wadanda harin ya rutsa dasu.
Cikin gaggawa aka tafi da wadanda suka ji raunin zuwa asibitin sojoji dake barikin sojin sama mallakin amurka mai suna US AL Udeid dake Qatar inda bada jimawa ba uku daga cikin su suka rasa rayukan su.
A ranar 1 ga watan yuli ne aka gudanar da jana’izar laftanal kanal james c. williams a garin sa na haihuwa dake New Mexico inda aka binne shi makabartar a Fe santa kamar yadda Everloved ta tabbatar.
Sai dai sanarwar mutuwar james bata fayyace dalilin mutuwar sa ba domin an boye cewa ya mutu ne sakamakon harin soji.
A wannan ranar da aka bizne babban jami’in sojin isra’ila babban kanal Sharon Asman a makabartar Kfar Yona a garin su.
Manyan sojin amurka sun sha rasa rayukan su a yankin gabas ta tsakiya, ko a shekarar 2014 ma mutuwar Janaral Harold Greene a afghanistan ta dauki han kalin manema labarai.
Makamantan hakan sun sha faruwa a shekaru amma amurkan takan rufe labarin domin gudun shan kunya a idon duniya.
Harin dai wanda kungiyar ‘yancin iraki ta aiwatar ramuwa kan harin da amurkan ta kai kan iyakar iraki da siriya inda ta kashe mambobin kungiyar da dama.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin amurka ta boye dalilin mutuwar lt. kanal james inda tace ya mutu ne a dalilin rashin lafiya.
Shuagaban kasar amurka ya bukaci karin bayani na na musamman a kan kungiyar ta neman ‘yanci iraki.
An kuma tabbatar da cewa an boye lamarin daga majalisar kasar ta amyrka.