Dangane da batun da ake ta yadawa a kafafan yada labarai na cewa gwamantin jihar kaduna ta shirya daukaka kara bayan kayen da ta sha a shari’ar ta da babban malamin nan shugaban mazahabar shi’a na afirka malam Ibrahim Zakzaky, mun tuntubi babban lauya kuma daya daga cikin lauyoyin da sukayi uwa sukayi makarbiya tsawon sama da shekara uku tun daga soma shari’ar har zuwa kammalawa.
Barista Ishaq Adam wanda sananne ne a cikin lauyoyin malamin kuma yana daga daga cikin mambobin harka islamiyya wacce malamin yake jagoranta ya fayyace mana halin da ake ciki gami da fayyace mana mahangar doka dangane da batun daukaka karar da ake zargin gwamnatin ta kadun tayi.
Da farko babban lauyan ya tabbatar mana da cewa a matsayin su na lauyoyin malam basa tsoro ko shakkar duk wata daukaka kara ko shigar da sabuwar kara da gwamnatin ta jihar kadun zata shigar domin sun tabbatar sune zasuyi nasara sakamakon gwamnatin ta jihar kaduna bata da wasu hujjoji da ta tanada, sabanin bangaren masu wakiltar malam da yake suna da tarin hujjoji da suke tabbatar da malamin bai aikata laifin komi ba kamar yadda kotu ta tabbatar har a karo biyu.
Daya juya batun daukaka karar ya tabbatar da cewa zuwa yanzu a matsayin su na lauyoyin malamin basu karbi wata takarda ta shari’a daga kowanne bangare ba, ya kuma kara da cewa babbar kotun daukaka kara ta gwamnatin tarayya da ake ta yamadidin nan aka kai karar alkalan ta suna hutu ne kuma ba zasu dawo ba sai bayan watanni biyu masu zuwa.
Lauyan ya tabbatar da cewa al’umma masoya, magoya baya, almajirai da masu fatan alkairi ga malam zakzaky su kwantar da hankulaun su domin koda gwamnatin kadunan ta daukaka kar ba yana nufin za’a kuma kama malam zakzaky bane, a hakika ma malamin baya bukatar halartar kotu illah lauyoyin sa da zasu dinga halartar kotu, yayin da shi kuma zai cigaba da rayuwaar sa kamar yadda ya saba ciki har da tafiye tafiye kasashen ketare ba tare da fuskantar kowacce irin matsala ba kamar yadda kundin tsarin mulkin najeriya ya tanada.
Ana sa ran dai malamin wanda yake fama da matsalolin lafiya shida mai dakin sa zasu shilla zuwa ketare domin tafiyar neman lafiya.