A Gambiya yau Laraba ne shugaba Adama Barrow zai yi rantsuwar kama aiki a sabon wa’adin mulki na biyu kuma na tsawon shekaru biyar.
Adama Barrow shi ne shugaba na uku da Gambiya ta gani tun bayan samun ‘yancin kai a 1965.
Shugabannin Afirka da dama ne ke halartar bikin rantsuwar a filin ‘yancin kai na Bakau.
A jawabin farko bayan sake zabensa a farkon watan Disamba, shugaba Adama Barrow, ya bayyana aniyar sabuwar gwamnatinsa na sake fasalin tsarin mulkin Gambiya, wanda zai iyakance wa’adin shugaban kasa.
A cewarsa, sabon tsarin mulkin zai kuma sake fasalin tsarin zaben kasar ta yadda zai kunshi batun zuwa zagayen zabe na biyu, idan ba a samu dan takarar da ya lashe kashi 50 cikin 100 na kuri’un da aka kada ba.
Adama Barrow, mai shekara 56 ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 53 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada.