Turkiyya ta ce ta shirya jerin sunayen majinyata 50 galibi yara kanana da za ta kwashe daga Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda aka shafe kwanaki 46 ana kai hare-hare ba kakkautawa.
Bayan da Turkiyya ta karbi rukuni biyu na jimlar marasa lafiya 88 daga yankin Falasdinawa da aka mamaye a cikin makonnin da suka gabata, Ministan Lafiya Fahrettin Koca ya ce za a iya kwashe na uku a cikin kwanaki masu zuwa.
Koca ya shaida wa ‘yan majalisar dokokin Turkiyya a majalisar dokokin kasar a Ankara babban birnin kasar cewa, “Za a iya kai dauki na uku a cikin kwanaki masu zuwa,” yana mai cewa kasra za ta fi ba da muhimmanci wajen kwashe jarirai da yara da marasa lafiya.
Ya ce tare da majinyatan 88, Turkiyya ta karbi jimillar mutane 150 daga Gaza da suka hada da abokai 62, ya ce majinyata shida na samun kulawa a sashen kula na musamman.
Da aka tambaye shi game da kwashe jarirai bakwaini a Gaza, sai ya ce suna shirin fara kwashe jarirai ‘yan kasa da watanni 12 da yara ‘yan kasa da shekaru hudu.
1432 GMT — Afirka ta Kudu ta zargi Isra’ila da aikata laifukan yaki da ‘kisan kare dangi’
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya zargi Isra’ila da aikata laifukan yaki da “kisan kare dangi” a Gaza, yayin da ya jagoranci wani babban taron kungiyar kasashen BRICS.
Pretoria tana karbar bakuncin taron BRICS – kungiyar manyan kasashe masu tasowa wadanda suka hada da Brazil da Rasha da Indiya da China, da Afirka ta Kudu – da nufin samar da martani daya ga rikicin Isra’ila da Falasdinu.
“Hukuncin gama-gari da ake yi wa Falasdinawa fararen hula ta hanyar amfani da karfi da Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba laifi ne na yaki. Hana magunguna da man fetur da abinci da ruwa ga mazauna Gaza da gangan, tamkar kisan kiyashi ne,” in ji Ramaphosa.
1353 GMT — Ana samun ci gaba a ‘yantar da mutanen da ake garkuwa da su a Gaza — Netanyahu
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce “muna samun ci gaba” kan dawo da mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a harin na ranar 7 ga watan Oktoba, bayan masu shiga tsakani sun ce ana shirin sasantawa.
“Ina fatan za a samu labari mai dadi nan ba da jimawa ba,” Netanyahu ya fadawa sojojin Isra’ila a wani sansanin soji da ke arewacin kasar
Jim kadan bayan haka, ofishinsa ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa, “bisa la’akari da ci gaban da aka samu dangane da sako mutanenmu da aka yi garkuwa da su”, majalisar ministocin yaƙi da na tsaro da kuma gwamnati za su yi taro a jere a yammacin ranar Talata.
Kalaman na zuwa ne bayan da shugaban Hamas da kuma babbar mai shiga tsakani Qatar duk suka ce akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar sulhu da Isra’ila.
1350 GMT — Isra’ila ta kashe ‘yan jarida biyu a kudancin Lebanon
Isra’ila ta kashe ‘yan jarida biyu wadanda suke aiki da gidan talabijin na Al-Mayadeen a yankin Tayr Harfa da ke kudancin Lebanon.
Gidan talabijin din ya fitar da sanarwa inda ya yi ta’aziyyar rasuwar wakiliyarsa Farah Omar da kuma mai daukar hotonta Rabie Al-Maamari.
Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya ruwaito firaiministan kasar Najib Mikati yana Allah wadai da kisan ‘yan jaridar.
A picture of the Al-Mayadeen TV photographer, Rabih Al-Maamari, and reporter, Farah Omar, who were killed this afternoon in an Israeli artillery bombardment in the village of Tayr Harfa in southern Lebanon. pic.twitter.com/8MdqQT2vBM
— Quds News Network (@QudsNen) November 21, 2023
Kamfanin dillancin labarai na Al-Quds da ke da alaka da Hamas ya wallafa hotunan ‘yan jaridar biyu a shafinsa na X.
1220 GMT — Duka asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki: ma’aikatar lafiya
Duka asbitoci a arewacin Gaza sun daina aiki, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar.
Ma’aikatar ta bayyana cewa a halin yanzu ana kokarin fitar da marasa lafiya da ke Asibitin Indonesia.
A bangare guda kuma ma’aikatar ta bayyana cewa akwai mutum 259 wadanda aka raunata, da farar hula da dama a cikin Asibitin Al Shifa kuma babu ranar kwashe su.
0920 GMT — Hezbollah ta dauki nauyin kai wani hari kan Isra’ila
Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta dauki nauyin wani hari da aka kai kan wasu gidajen da sojojin Isra’ila ke zama a Metulla da ke arewacin Isra’ila.
Hezbollah ta bayyana cewa ta kai wannan harin ne domin ramuwar gayya kan gidajen kai iyaka da Isra’ilar ta kai wa hari a kudancin Lebanon.
Source: TRTHausa