Hukumar tsabtace Sahihancin Magunguna da Abinci ta Ƙasa, NAFDAC ta ce shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju’a, ma’ana, mutuwar gaggawa.
Hukumar ta ƙara da cewa magungunan karfin maza kan haifar da cutar ɓarin jiki inda maza za su riƙa shan su domin su burge matan da su ke saduwa da su.
Darakta-Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗin a saƙon ta na Kirsimeti da sabuwar shekara.
Adeyeye ta nuna rashin jin daɗin ta game da yadda magungunan karfin maza su ka cika kasuwannin magani a faɗin ƙasar nan.
A cewar ta, yawancin irin magungunan ma ba su da rijistar NAFDAC ɗin.
“Shigo da su a ke yi ta ɓarauniyar hanya. Inda su na da rijista, to masu shigo da shi da masu sayarwa ba za su riƙa yin abin da su ke yi a kasuwanni, ka tuna, kafafen sadarwa da tituna ba,”
Haka-zalika, wannan kiran na Adeyeye ya zo ne a lokacin da NAFDAC ta ce ta ƙwace jabun magunguna da kayan abinci da darajar su ta kai naira biliyan 3 a filin kasuwar bajakoli a Legas.