Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammed Ali Pate, ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai rattaba hannu kan wata dokar domin rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya.
Duba Nan: Kaddamar Da Sabuwar Hukumar Kula Da Aikin Hajji Ta Kasa
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Laraba a wani taron manema labarai na ministoci wanda ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Mohammed Idris, ke jagoranta a Abuja.
Yayin da yake bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya karkashin gwamnatin shugaba Ahmed Bola Tinubu tun daga watan Mayun shekarar 2023, Pate ya ce, duk da ficewar da manyan kamfanonin magunguna na duniya suka yi daga kasar, gwamnati ta dukufa wajen rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a kasar nan.
Ya ce, “wata doka ta Shugaba Tinubu na nan tafe don rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a kasar nan.”
A wani labarin na daban gwamnatin Tarayya da hadin gwiwar Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund), za ta samar da cibiyoyi fiye da 24 na fasaha da kirkire-kirkire a fadin Nijeriya don baiwa ‘yan Nijeriya damar bunkasa sana’o’insu.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a Abuja, lokacin da ya kai ziyara cibiyar Innov8 Hub, tare da masu ruwa da tsaki ciki har da babban sakatare na TETfund, Arch. Sonny Echono.
Innov8 cibiya ce mai horar da matasa fannin kirkire-kirkire da Fasahohi.
Mammam ya ce shirin samar da cibiyoyin fasaha fiye da 24 a fadin kasar nan, an yi shi ne don baiwa matasa ‘yan Nijeriya damar samun sana’o’i da fasahohi a bangarori daban-daban.