Faransa ta gabatar da wani tsarin fadada shirin tazarar iyali da ya sahalewa mata ‘yan kasa da shekaru 25 karbar kwayoyin hana daukar ciki kyauta kuma cikin sauki a wani yunkuri na dakile kananan yaran daga daukar ciki baya ga hana su karaya daga shan magungunan saboda tsadarsu.
Kwayoyin hana daukar ciki ga kananan yara dai kyauta ne a kasashen Turai irinsu Faransar da Belgium da Jamus da Netherlands da Norway yayinda Birtaniya ke bayar da shi hatta ga manya ba tare da kudu ba.
A watan Satumba ne Faransa ta sanar da shirin kara yawan wadanda za su ci gajiyar kwayoyin kyauta zuwa har ‘yan shekaru 25 saboda yadda tsadarsu ke hana matan siya kuma suke karewa da daukar cikin da basu shiryawa ba.
A cewar ma’aikatar tattalin arziki ta Faransar, ta bakin kakinta Louise Delavier matakin kara masu cin gajiyar kyautar kwayoyin hana daukar cikin na da nasaba da yadda alkaluma suka nuna musu wahalhalun da mata ke haduwa da su ta fuskar tattalin arziki idan suka haifi ‘ya’yan da basu shirya musu ba.
Amma sai dai masu nazarin lamurra suna ganin gwamnatin faransan na goyon bayan yawaita saduwa da kananan yara kafin aure ne gami kuma da zubar da ciki.