Rahoton da kungiyar ta fitar yau alhamis ta ce jami’an Sojojin na Mali sun azabtar da mutanen 6 ta hanyar amfani da munanan hanyoyi ciki har da jona musu lantarki da tsoma su a ruwa kana duka marar misaltuwa.
Kungiyar ta bayyana cewa yanzu haka mutanen 6 na tsare a wani sansani da baya jerin halastattun gidajen yari ko wuraren tsare jama’a da jami’an gwamnatin kasar ke da su, yayinda su ke fuskantar azabtarwa.
A cewar kungiyar fitar da rahoton na ta ya biyo bayan tattaunawa ta wayar tarho da akalla bangarori 3 da suka kunshi Iyalan mutanen da lauyoyi da kuma mambobin hukumar kare hakkin dan adam ta kasar.
Kungiyar ta Human Right Watch ta bayyana cewa ta na da hotuna da ke tabbatar da zargin na ta a kan jami’an tsaron kasar.
A wani labarin na daban kuma shugabanin kasashen ECOWAS za su gudanar da wani taro na musaman dangane da makomar kasashen Guinee da Mali wadanda sojoji suka yi juyin mulki wajen kifar da gwamnatocin fararen hula a cikin su.
Tuni kungiyar ECOWAS ta dakatar da wadannan kasashe daga cikin ta tare da gabatar da bukatar shirya zabe domin mayar da mulki ga fararen hula.
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Johnatan mai rike da mukamin manzon kungiyar ECOWAS ya gana da shugabanin majalisar sojojin dake rike da mulki a kasashen Mali da Guinee ba tare da cimma matsaya dake tabbatar cewa sojojin na shirye don yin aiki da shawarwarin kungiyar Ecowas da za ta kai su ga shirya zabuka ba kamar yadda aka bukata.
Ita ma kungiyar Afirka ta AU ta bi sahun ECOWAS wajen dakatar da wadannan kasashe daga cikin ta.