Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta bayyana wannan alkawarin mai dadi inda tace zata gwangwanje duk wanda ya fallasa masu boye kudi da kyauta mai tsoka.
Wannan alkawarin yana zuwa ne yayin da ake sauya kudin kasar Najeriya bayan shekaru 15 inda za a samu sabbin kudade a kasar.
Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC tayi alkawarin kudi mai tsoka ga duk wanda ya fallasa wani wanda ke boye tsabar kudi.
Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, ya bayar da wannan tabbacin yayin zantawa da gidan rediyon Hausa na Deutsche Welle a ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba.
FG Ta Kara Kudi Kan Filet din Kowanne Abincin Dalibai Kamar yadda Bawa yace, za a bai wa mai kwarmato kashi biyar na dukkan kudin da aka samo, ICIR ta rahoto.
Shugaban EFCC din yayin bayani kan sake sauya fasalin Naira, ya jaddada cewa wannan yunkurin na Babban bankin Najeriya bashi da alaka da siyasa amma gwamnati tana son tirsasawa wadanda suka boye kudi a gida kan su fito dashi su zuba a asusun bankunansu.
“Muna kira ga ‘yan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba kan cewa dukkan kofofi a bude suke.
Idan wani ya san wanda ya boye kudin da ake zargi, su fallasa kuma mu zamu bincika. “
Idan mun bincika kan kudin tare da samo su, mai kwarmaton zai samu kashi biyar daga ciki.
“Wadannan kudin an wawure su ne kuma muna so a dawo dasu. Ba mu hana kowa fito da kudi ba.
Abinda gwamnati tace shi ne a zuba kudi asusun bankuna ko hukunci ya biyo baya.”
A yayin yanko tanadin shari’a, shugaban EFCC din yace sauya fasalin naira din ana tsammanin za a dinga yin shi duk bayan shekaru takwas. “
Najeriya ta kwashe shekaru 20 bata sauya kudinta ba, kusan kashi 80 na naira basu bankunan ‘yan kasuwa da CBN, suna hannun jama’a. “
Toh ta yaya gwamnati zata yi nasara? Ta yaya kasar zata samu kashi 25 na cinikayya da kasashen ketare wanda zata amfana dsa kudin kasar cikin kwanaki 10?”
EFCC ta kai samame kan ‘yan canji Bayan bayyana cewa za a canza fasalin Naira, kasuwar canji ta bude inda Naira ta fara tashin gwauron zabi.
Hukumar EFCC bata yi kasa a guiwa ba ta kai samame madaddalar ‘yan canji dake babban birnin tarayya a Abuja.
Source:Legithausa