A Burkina Faso, dubban magoya bayan tsohon Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ne suka fito zanga zanga don nuna damuwar su ganin ci gaba da tsare tsohon shugaba da majalisar sojin kasar ke yi yanzu haka.
Magoya bayan tsohon Shugaban sun gudanar da zanga-zangar lumanar ce a birnin Ouagadougou.
Yayin jawabi ga manema labarai sun gargadi majalisar sojin kasar da ta gaggauta kawo karshen tsare tsohon Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore da aka kifar ranar 24 ga watan janairun shekarar nan, mudin hakan ba ta samu ba to za su fadada wanan zanga-zanga zuwa sauren yankunan kasar ta Burkina Faso 45.
Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ta Ecowas ta shiga tattaunawa da majalisar sojin kasar ta Burkina Faso,na ganin lamura sun daidata,tun bayan juyin mulkin watan janairu,ba tareda cimma wani muhimin sauyi ba yanzu haka.
A wani labarin na daban birnin Shanghai a China ta sanar da mutuwar mutane 39 da cutar covid-19 ta kashe a yau Lahadi, adadi mafi yawa duk da da makonni da aka shafe ana kulle, a yayin da mahukuntan birnin Beijing suka yi gargadin cewa akwai yiwuwar ta’azzarar yaduwar cutar
Kasar, wadda ita ce ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya, tana ta kokarin shawo kan annoba mafi muni da ta addabe ta a cikin shekaru 2, inda ta yi ta kakaba dokokin kulle masu gauni, tare da gwaji ba kakkautawa.
Birnin Shanghai, wanda shine cibiyar kasuwancin China ya shiga yanayi na kulle a gaba daya watan da ya gabata, lamarin da ya sa mazauna garin zama a gida na tsawon lokaci fiye da yadda suka taba yi.
Birnin mai yawan al’umma miliyan 22, ya na ta kokarin samar da abinci mai inganci ga wadanda ke kulle a gidaje, a yayin da marasa lafiya keta korafin rashin samun kulawa, sakamakon yadda aka aike da dubban malaman lafiya zuwa cibiyoyin gwaji da kula da masu Covid-19.