Mazauna kauyukan karamar hukumar Bakura dake Jihar Zamfara a Najeriya na zaman makoki sakamakon kisan gillar da Yan bindiga suka yiwa mutane sama da 50 a wani kazamin hari da suka kai musu a karshen mako.
Yan bindigar sun afkawa asibiti garin Damri,inda suka kashe masu jinya tareda kona motar yan Sanda .Da samun labarin wannan hari,an tura sojoji,wandada suka samu nasarar korar yan bindigar.
Jihar Zamfara na ci gaba da fama da matsalar tsaro sakamakon hare haren Yan bindiga wanda ya kaiga rasa dubban rayuka a kasar.
A wani labarin na daban Al’amurra na ci gaba da zafafa tsakanin bangarorin jamiyyar APC na jihar Zamfara akan batun zaben sabbin shugabannin jamiyyar a matakai daban daban na jihar, a yayin da bangaren Sanata Kabiru Marafa ke ci gaba da gudanar da zaben shugabannin a karkashin kulawar bangaren tsohon gwamna Abdulaziz Yari.
Dama dai shugaban riƙo na APC a jihar Zamfara da ke a bangaren Abdulaziz Yari Lawal M Liman ya shaida wa magoya bayansu cewar su nisanci taron zaben (Congress) da bangaren gwamna Bello Matawalle suka bayyana shi a matsayin taron da bashi akan doka.
A wannan Assabar ma taron na zaben shugabannin kananan hukumomi a jihar ta Zamfara ya rabu gida biyu yayin da bangaren gwamna Matawalle a karkashin jagorancin Alhaji Hassan Nasiha sun gudanar da nasu taro yayin da bangaren Kabiru Marafa suma ke nasu duk a wuni guda.
Sanarwar bangaren Yari
A wata rubutacciyar sanarwa da bangaren tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya fitar wannan Assabar dauke da sa hannun Ibrahim Dan Madamin Birnin Magaji, bangaren na tsohon gwamna na cewar sun bukaci magoya bayansu su zura ido ne kawai suna masu dogaro da cewar yanzu haka akwai shara’a a gaban babbar Kotun tarayya dake nan Gusau kan wannan taro don haka ba za su shiga taron ba har sai Kotu ta gama yanke hukunci akai.
A bisa haka inji sanarwar bangaren Abdulaziz Yari ya zabi ya bi ka’ida wajen mutunta umurnin Kotu. Dama dai Alkalin Kotun Justice Aminu Bappa ya dage zaman Kotun har zuwa ranar biyu ga watan Disamba domin yanke hukunci.
Bangaren Matawalle
To ko me bangaren gwamna Matawalle zasu ce dangane da wannan, tambayar da muka yi wa Gado Sony wani makusancin gwamna Matawalle ta wayar tarho ya kuma ce baida abinda zai ce, a yayin da Hassan Nasiha wanda shine shugaban rikon kwarya na APC a bangaren gwamna Matawalle bai dauki kira ba bai kuma maida sakon kar-ta-kwana na wayar Tarho da muka aika masa ba.
To sai dai a ta bakin Bello Bakyasuwa mai magana da yawun Sanata Marafa a zantawarmu ta wayar tarho, sun dauki matakin yin nasu taron ne domin nuna wa uwar jamiyyar cewa ba zasu bari wadanda ba cikakken ya’yanta ba, su wargaza mata tsari. Amma a cewar sa, duk da haka su masu ladabi ne ga umurnin kotu, sannan daukar matakin yin taron da suka yi ba yana nufin suna da matsala ne da ubangidansu tsohon gwamna Abdulaziz Yari ba ne.