Karim Benzema yana da yakinin cewa zai samu kuzarin da zai fafata a wasan kungiyarsa, Real Madrid da Paris Saint-Germain a wasan gasar zakarun nahiyar Turai in an jima a Talatar nan, bayan da ya yi jinyar rauni a kafarsa.
A jiya Litinin dan wasan gaban na Real Madrid ya shaida wa manema labarai cewa ya ji garau, kuma yana jin cewa za a iya damawa da shi.
Benzema, wanda shine dan wasan da ya fi kowa saka kwallaye a raga a Real Madrid, inda ya ci kwallaye 24 a dukkan gasa, bai buga wa kungiyarBenzema, wanda shine dan wasan da ya fi kowa saka kwallaye a raga a Real Madrid, inda ya ci kwallaye 24 a dukkan gasa, bai buga wa kungiyar tasa wasanni 3 ba tun bayan da ya fita daga fili yana dingishi a wasan da suka barje gumi da Elche 2-2 a ranar 23 ga watan Janairu.
Benzema ya ce fafatawarsa da kylian Mbappe a bangaren PSG wani abu ne na musamman a gareshi, duba da yadda ake ta rade radin zai koma Madrid, da kuma ganin cewa dukkanninsu su na yi wa tawagar Faransa wasa.
Bangarorin 2 za su hadu ne a filin wasa na Parc des Princes, kana su yi fafatawa ta 2 a Madrid ranar 9 ga watan Maris.
A wani labarin na daban Wani binciken masana ya nuna cewar canjin yanayi ya sauya lokacin da ake samun ambaliyar ruwa a Turai, inda ake samun wasu koguna na cika da wuri, wasu kuma a makare, abinda ke matukar illa ga ayyukan noma da rayuwa baki daya a Yankin.
Farfesa Guenter Bloeschi na Jami’ar Fasaha ta Virginia da ya jagoranci binciken, ya ce a kasashe irin su Sweden da Findland da Yankin Baltic, a kan samu ambaliya wata guda kafin yadda aka saba gani a shekaru 1960 da 1970.
Shehun malamin ya ce a wancan lokacin a kan samu matsalar ce a watan Afrilu, amma a yau ana samu ne a watan Maris saboda narkewar dusar kankara da wuri.