A Faransa ,kusan wata daya da rabi da gudanar da zaben Shugaban kasar, da ya baiwa shugaba mai ci Emmanuel Macron nasarar lashe zaben , a yau lahadi aka fara zaben yan majalisun dokokin kasar.
Zaben Faransa na yau na a matsayin zakaren gwajin dafi ga Shugaba Emmanuel Macron,wanda a karkashin jam’iyya mai mulkin kasar zai yi kokarin ganin ya samu rinjaye a majalisar dokokin Faransa,wanda shaka babu hakan zai bas hi damar tafiyar da manufofin da yake da su ta fuskar siyasa kamar yada ya dau alkawali a yakin neman zaben da ya gabata.
Shugaban kasar Emmanuel Macron na ci gaba da fuskantar suka daga wasu yan siyasa da Faransawa dake kalon sa a matsayin mutumen da ya durkusar da diflomasiyar Faransa a idanun Dunitya,yayinda masu goyan bayan sa ke ci gaba da kawo ta su goyan baya a siyasar Shugaba Emmanuel macron.
Sama da Faransawa milyan 43 ne suka karbi katunan zabe domin sabinta wannan majalisa mai dauke da yan majalisu 577 inda ake da yan takara sama da dubu 6, zaben da za aje zagaye na biyu ranar 19 ga watan yuni.
A wani labarin na daban jami’an diflomasiyyar Faransa za su shiga yajin aiki a wata mai zuwa, karo na biyu a tarihin kasar, a wani yunkuri na nuna rashin amincewarsu da sauye-sauyen gwamnati da kungiyoyin kwadagon suka ce zai kawo cikas ga ma’aikatar harkokin wajen kasar a dai dai lokacin da duniya ke cikin halin tsaka mai wuya.
Babban abin da ya haifar da korafin shi ne batun sake fasalin tsarin aiki wanda zai tabbatar da ganin an soke matsayi na musamman da aka baiwa manyan jami’an diflomasiyyar daga shekara mai zuwa, a cewar kungiyoyin kwadago na kasar.
Kungiyoyin suka ce wadannan matakai na rusa aiyukan diflomasiyya bazaiyi tasiri ba, a dai dai lokacin da yake yake suka mamayi Yankin Turai, cikin wani sakon hadin gwiwa da kungiyoyin suka fitar.
Cikin sauye-sauyen da Shugaba Emmanuel Macron ya gabatar aka yi gaggawar aiwatar wa, bisa doka a watan Afrilu, manyan jami’an ma’aikatar harkokin waje za su rasa matsayinsu na musamman kuma za’a tsunduma su cikin jiga jigan ma’aikatan gwamnati shafaffu da mai.
Yin hakan na nufin za’a tura manyan jami’an Diflomasiya a kalla 700 wasu ma’aikatu da basu shafi bangaren diflomasiya ba don cigaba da gudanar da aiyukan su.
Yayin da wani jami’in diflomasiyar da ya yi magana ba tare da baiyana sunan sa ba ya baiyana cewar sun kasance cikin matukar damuwa domin ba’a sauya matsayin su na aiki amma yana daraja abokan aikin sa na sassan a kasar domin bai san yadda zai gudanar da irin aiyukan su ba suma kuma basu san nasa ba.
Faransa ce dai kasa ta uku mafi girma a harkokin kasashen ketare a duniya bayan China da Amurka, tare da ma’aikata kusan 14,000 a ma’aikatar harkokin waje gaba dayan ta.
Wannan yajin aikin dai za a fara shi ne a ranar 2 ga watan yuni.