Masu aikin ceto a Brazil na cigaba da neman masu sauran rai cikin laka da baraguzan gine-gine, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa, da zabtarewar kasa a birnin Petropolis, a daidai lokacin da kawo yanzu adadin yawan wadanda suka mutu a iftila’in ya karu zuwa mutane 117
Guguwar dai ita ce ta baya bayan nan da ta afkawa Brazil cikin watanni ukun da suka gabata, masifun da masana suka ce sauyin yanayi ne ke kara ta’azzara su.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta Petropolis ta ce an ceto akalla mutane 24 da ransu.
Da farko an ce, ana fargabar kimanin mutane 300 sun bace sakamakon wannan ibtila’in na ranar Taklatar nan.
Masana sun bayyana cewa, ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.
A wani nlabarin na daban Hukumar Lafiya ta Duniya tace akalla jami’an kula da lafiya 115,500 suka mutu sakamakon harbuwa da cutar korona a cikin watanni 18 da suka gabata.
Daraktan dake kula da lafiyar wuraren aiki da kuma sauyin yanayi a hukumar lafiya, Maria Neira ta ce wuraren ayyukan yi kadan ne ke da matakan kariyar dake kare ma’aikatansu a wuraren da suke aiki.
Neira ta ce ma’aikatan lafiya sun gamu da matsaloli da dama da suka hada da cututtuka masu yaduwa da samun raunuka da cin zarafi da kuma rashin ingancin wuraren aik