Yawan mutanen da suka kamu da cutar Korona a fadin duniya ya zarta miliyan 300, kamar yadda alkaluman hukumomin lafiya suka nuna a ranar Juma’a.
A cikin kwanaki bakwai da suka gabata dai, akalla kasashe 34 ne suka ba da rahoton gano adadin masu kamuwa da Korona mafi yawa, yanayi mafi tsanani da suka gani tun bayan barkewar annobar a shekarar 2020.
Daga cikin kasashen da suka fuskanci hauhawar ta masu Korona 18 na Turai, yayin da 7 ke nahiyar Afirka, kamar yadda alkaluman da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara daga hukumomi.
A karshen makon nan shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadin cewa bai kamata a sanya Omicron cikin nau’in Korona marar tsanani ba, domin kuwa yana kwantar da mutane a asibiti gami da kashe wasu da dama.
A labarin na daban kuma a Wani rahoton hadin gwiwa tsakanin hukumar lafiya WHO da Bankin Duniya ya nuna yadda cutar covid-19 ta haddasa gagarumar matsala ta fuskar ci gaba da kuma koma bayan akalla shekaru 20 wanda ya kai ga jefa mutane fiye da miliyan 500 cikin matsanancin talauci dai dai lokacin da jama’a ke fuskantar matsala da kuma tsadar kula da lafiya.
Rahoton hukumomin biyu ya buga misali da yadda cutar ta covid-19 ta yi kokarin gagarar bangaren lafiyar hatta kasashen da suka ci gaba a shekarar 2020, duk da kokarin shawo kan annobar.
Sabon rahoton na WHO da Bankin Duniya ya kuma yi gargadin kan yadda matsalolin tattalin arziki ke ci gaba da tsananta a bangare guda kuma al’umma ke kara talaucewa saboda katsewar hanyoyin samu da kuma tsadar rayuwa baya ga gazawar gwamnatoci.
Acewar WHO kafin covid-19 kashi 68 cikin 100 na al’ummar duniya sun samu sassaucin kiwon lafiya, musamman bangaren kula da mata masu juna biyu da ayyukan rigakafi da yaki da cutukan HIV da tarin TB da ma saukin magungunan cutuka marasa yaduwa irin su daji, ciwon zuciya da kuma ciwon sukari.
Sai dai rahoton hukumomin biyu ya ce, bullar covid-19 ta tsawwala harkokin kula da lafiya wanda zai zamewa mutane gagarumar matsala a yanzu.