Dakarun gwamnatin Habasha da wasu kungiyoyin yan kato da gora sun kaddamar da farmaki zuwa yankunan yan tawayen Tigray a yankin Amhara dake kan iyaka da fagen daga a arewacin wanna kasa.
Mai magan da yahun yan tawayen TPLF Getachew Reda dake fada da dakarun gwamnati tsawaon watanni 11 sun shirya wajen shiga yakin gadan-gadan.
A wani labarin na daban lkitoci da jami’an Amhara sun ce an kashe fararen hula sama da 120 a yankin da ke kasar Habasha a farkon wannan watan.
Sai dai cikin sanawar da suka fitar ‘yan tawayen Tigray sun yi watsi da abin da suka kira labarain da da gwamnatin yankin Amhara ta kirkira.
‘Yan tawayen na Tigray sun kuma musanta a hannu a kisan fararen hular fiye da 100.
Tun daga watan Nuwamban shekarar 2020, arewacin kasar Habasha ke fama da rikice-rikice, lokacin da Fira Minista Abiy Ahmed ya tura sojoji zuwa Tigray don kawar da jam’iyya mai mulkin yankin ta TPLF, matakin da ya ce martani ga hare-haren da mayakan ‘yan tawayen TPLF ke kaiwa sansanin sojoji.