‘Yan sandan Faransa, sun kama mutane 97 da suka karya dokar da ta hana zanga-zangar kin amincewa da ka’idojin coronavirus tare da hana zirga-zirga a birnin Paris, yayin da 81 har yanzu ke tsare.
Rundunar ‘yan sandan birnin Paris ta kuma ce an bude wani bincike na cikin gida bayan wani faifan bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta da ke nuna wani jami’in dan sanda ke nuna bindigarsa a kan wani direba.
Sama da motoci 400 ne suka yi sansani a wurare da dama da ke kusa da birnin Paris cikin dare, kuma masu shirya zanga-zangar sun yi kira ga mutane da su nufi Brussels don wata babbar zanga-zanga a yau Litinin, kamar yadda majiyar ‘yan sandan kasar ta Faransa ta tabbatar.
A wani labarin na daban An diga ayar tambaya kan tsarin bai wa shugaban Faransa Emmanuel Macron tsaro bayan wasu masu zanga-zanga sun tunkare shi kai-tsaye a yayin da yake tattaki tare da matarsa a wani lambu da ke birnin Paris.
Wani hoton bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda masu zanga-zangar ke yi wa shugaban ihu, suna masu fadin cewa, “ Macron demission” ma’ana Macron ka yi murabus, yayin da masu boren suka yi wa tawagar shugaban kuri.
Ala tilas dai, shugaban na Faransa ya tanka masu zanga-zangar da suka yi ta nuna masa yatsa a fuska tare da yi masa korafi kan rashin daidaito a bangaren tattalin arziki da kuma yadda jami’an ‘yan sanda ke amfani da karfi kan masu bore.
An dai jiyo shugaban na Faransa na mayar musu da martani kai-tsaye, yana mai cewa, “ ku sassauta” yayin da ya kasa kunne yana sauraren korafinsu.
Shugaban ya ce musu lallai ya fahimci kuncin da suke ciki, duk da dai ya ce, akwai masu tayar da hargitsi a tsakaninsu, lamarin da ya sa ‘yan sanda ke nuna musu karfi.
Babu dai wanda ya sanya kyallen rufe fuska tsakanin Macron da masu zanga-zangar a yayin musayar kalamai tsakanin bangarorin biyu.
A bangare guda, jagoran jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi a Faransa, Jean-Luc Melenchon ya ce, ya kamata Macron ya yi taka-tsan-tsan a matsayinsa na shugaban kasa wajen gudanar da irin wannan tattaki a yankin da ya-ku-bayi ke da rinjaye.