Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin ‘yan gudun hijirar da suka tsere daga Ukraine bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar ya haura dubu 400 a dai dai lokacin da kungiyar EU ta yi hasashen cewar, adadin ‘yan Ukraine din da za su rasa muhallansu ka iya zarta miliyan 7, sakamakon yakin da ke gudana.
Tun kafin yakin da Rasha ta kaddamar dai, dama Poland ta kasance mafaka ga ‘yan Ukraine akalla miliyan 1 da rabi.
A cigaba da kokarin da wasu kasashe ke yi na taimakawa Ukraine kuwa, Amurka ta sanar da aikewa da kusan dala miliyan 54 a matsayin sabon taimakon jin kai ga Ukraine a dai dai lokacin da ta ke fama da mamayar Rasha.
Sakkataren harkokin wajen Amurkan Anthony Blinken ya ce taimakon ya hada da “samar da abinci da tsaftataccen ruwan sha da kuma matsuguni kana kula da ayyukan kiwon lafiya na gaggawa.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO kuwa, ta yi kira ne da a samar da amintacciyar hanya daga Poland don isar da kayayyakin agajin kula da lafiya ga Ukraine, inda ta yi gargadin cewa tukwanen iskar oxygen na gaf da karewa a asibitocin kasar.
Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadin cewa tukwanen na iskar oxygen ka iya karewa a yawancin asibitocin Ukraine cikin sa’o’i 24.