Kunzumin Yahudawa bakin haure ‘yan share wuri zauna ne suka yi tattaki a Birnin Kudus dauke da tutar Israila matakin dake harzuka Falasdinawa shekara guda bayan irin wannan tankiyar ta haifar da yaki.
Yahudawa da yawan su suka shiga tattakin na jiya akan titunan Birnin Kudus dauke da tutar haramtacciyar kasar su, yayin da suke samun rakiyar jami’an Yan Sanda, tattakin dake nuna mamaye Gabashin Birnin Kudus da haramtacciyar kasar israila tayi, tare da kashe wani adadi na larabawa yan asalin yankin wanda haramtacciyar kasar ta Israila tayi a shekarar 1967.
Kisa ga larabawa
Wasu daga cikin masu tattakin sun yi ta shelar ‘Kisa ga Larabawa‘, yayin da wasu Falasdinawa suka tanka musu daga kan gidajen su amma hakan ya sanya falasdinawan sun hadu fushin jami’an ‘yan sandan haramtacciyar kasar ta israila wadanda ke rakiyar yajudawan yan share wuri zauna.
Ministan harkokin wajen Israila Yair Lapid ya bayyana kungiyoyin Yahudawan masu tsatsauran ra’ayi dake takalar Larabawa musamman a Lehava da La Familia dama sauran sassa a matsayin babban abin kunya, wadanda bai dace su dauki tutar haramtacciyar kasar israila.
Tinzira tashin hankali
Firaministan Israila Naftali Bennet ya umurci Yan Sanda akan cewar kar su kuskura su ragawa Falasdinawa masu tsatsauran ra’ayin dake neman tinzira tashin hankali a La Familia, a cewar sa.
Akalla Yan Sanda sama da 3,000 aka jibge a Birnin Kudus, yayin da aka kama falasdinawa sama 60 wadanda sukayi kokarin kare mutuncin mata da kananan yara, yayin da kungiyar agaji ta Red Cross tace Falasdinawa da dama suka samu raunuka a ciki da wajen Tsohon Birnin Kudus.
A wani labarin na daban gwamnatin Brazil tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon ruwan saman da aka shatata makon jiya ya kai 79, yayin da wasu da dama suka bata.
Fereira yace, mutane da dama sun bace, kuma wasu 25 sun samu raunuka, yayin da 3,957 suka rasa muhallan su.
Ministan yayi gargadin cewar suna fuskantar Karin ruwan sama a yankin, saboda haka aka bukaci mutane su zauna cikin shirin ko ta kwana.
Wannan dai shi ne iftila’i na baya bayan nan a cikin jerin bala’o’i da suka hada da zabtarewar kasa da ambaliyar ruwa da suka haifar da matsanancin yanayi a Brazil.