Najeriya; NCDC Ta Tabbatar Da Kamuwar Mutane 21 Da Cutar Kyandar Biri.
Hukumomin kiwon lafiya a tarayyar Najeriya sun tabbatar da kamuwar mutane 21 da cutar kyendan biri daga farkon wannan shekara zuwa yansu.
Hukumar NDCD mai yaki da cututtuka masu yaduwa ta bayyana cewa daga cikin mutane 61 da suke hasashen suna da alamun cutar, 21 sun kamu da ita, a yayin da daya daga cikinsu dan shekara 40 aduniya ya rasa ransa saboda cutar.
An saba samun cutar kyendan biri a kasashen Kamaru, Afirka ta tsakiya, Democdiyyar Kongo da kuma Najeriya a baya.
READ MORE : Iran Ta Yi Kira Ga Hadin Kai Don Fada Da Mulkin Wariya Na Isra’ila.
Amma cutar ta fara jawo hankali a lokacinda mutane kimani 200 sun kamu da ita a kasashen 19 a nahiyar Turai a cikin watan mayun da muke ciki,amma babu wanda ya mutu.
READ MORE : Gwamantin Mulkin Soji Ta kasar Sudan Ta Janye Dokar Ta Ba ci Da Ta Sanya A Kasar.
RAD MORE : Shugaban Kasar Tajikistan Ya na Ziyarar Aiki Ta Yini Biyu A Birnin Tehran.