Kamar yadda aka shaida kfofin sada zumunta na WhatsApp, Instagram da Facebook sun shafe tsawon awanni shida basa aiki, wanda hakan ya jefa mutanen da ake amfani da su cikin damuwa.
Shafuka da manhajojin WhatsApp, Instagram da Facebook wadanda dukkanninsu mallakin kamfanin Facebook ne, wanda kuma shi ke gudanar da su, sun daina aiki ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin.
Shafin WhatsApp wanda ake amfani da shi ta intanet, shi ne na farko da ya daina aiki kafin daga bisani manhajar ta waya ya daina; sannan Facebook da Instagram suka bi sahu.
Masu amfani da manhajoji ko shafukan WhatsApp, Instagram da Facebook, sun kasa turawa ko karbar sakonni ta nan, amma sauran kafafen sada zumunta irin su Twitter, TikTok, da Telegram suna aiki babu wata matsala.
Wannan shi ne karo na biyu da kafafen suka daina aiki a cikin kasa shekara guda, ko a ranar 19 ga watan Maris 2021, kafafon sun samu irin wannan matsala inda suka daina aiki har na tsawon sa’a biyu.
A wani labarin na daban duk da cewa addinin muslunci yana daga cikin addinai masu mabiya ‘yan tsiraru a kasar Japan, amma kuma a lokaci ana baiwa addinin musluci muhimmanci matsayi na musamman a kasar.
Ma’aikatar bunkasa al’adu da kula da ayyukan bude a kasar Japan, ta sanya masallacin Shizuoka a matsayin daya daga cikin muhimamn wurare a kasar, wadanda masu zuwa yawon bude ido za su iya ziyartar wurin.
Wanann masallacin da ake kira da koren masallaci ko kuma Green Mosque, yana daga cikin wurare na musulmi wanda aka yi amfani da fasaha ta musamman wajen gininsa da ke daukar hankula matuka.
Akasarin msuulmin da suke rayuwa a kasar Japan dai sun zo ne daga kasashe daban-daban, musamman kasashen larabawa da kuam kasashen gabashin Asia, gami da kadan daga cikin mutanen kasar wadanda suka karbi addinin muslunci.
Musulmi suna rayuwa a cikin ‘yanci na gudanar da dukkanin harkokinsu na addini ba tare da wata tsangwama ko cin zarafi, ko kuma nuna musu banbanci ba.