Yaƙin Ukraine; Rasha na cigaba da luguden wuta da kashe fararan hula.
Majiyoyin tsaro daga birnin Washington na Amurka na cewa dakarun Rasha na ci gaba da danna kai Ukraine sai dai sojojin Ukraine na kokarin wajen nuna jajircewa a yakarsu.
Sun ce har yanzu Rasha ba ta samu cikakken ikon sararin samaniyar Ukraine ba, sannan jeren gwanon sojojinta da suka doshi birnin Kyiv na maƙale wurin guda.
Manyan jami’an tsaro sun ce ana samun sauye-sauye a salon yaƙin Ukraine. Bayanan da suke samu na nuna cewa dakarun Rasha na ci gaba da kokarin matsa ƙaimi a yankunan arewaci da gabashi, sai dai suna fuskantar turjiya mai karfi daga Ukraine.
Bayanan da aka tattara kawo yanzu na nuna cewa an cimma kaso 95 cikin 100 na jami’an da Rasha ta jibge kafin soma mamayar.
Sannan ana ci gaba da gumurzu kan iko da sararin samaniya, kuma kowanne ɓangare ya yi asarar jiragen yaƙi da na’urorin kariya daga makamai masu linzami.
Majiyoyi na cewa zuwa yanzu Rasha ta harba makamai masu linzami kusan 600 tun daga soma yakin.
Akwai biranen Uku da ke arewa maso yammaci Kyiv – Bucha da Hostomel da Irpin da ake ci gaba da yiwa luguden wuta. Fararen hula da ke kokarin tserewa na rasa rayukansu.
Wata Uwa da yaranta biyu sun mutu yayinda aka jikkata mijinta. An tarwatsa gadar da mutane ke ratsawa domin tserewa ta kan wani kogi.
Wani jami’in Sojan Ukraine, Leutenan Oleg ya ce dakarun Rasha na gab da ci musu amma a cewarsa ba za su miƙa wuya ba.
Ya ce “makiyanmu ba su wuce tazarar kilomita biyar ba damu, suna ci gaba da luguden wuta, jiya harda makaman artillary suka rinka harba mana, yau da ɗan sauki, sai dai suna cigaba da jefa mana nakiyoyi babu kaukautawa.
Suna lalata gidaje, yakin akwai ban tsoro, sai dai ba zamu karaya ba.”
Mataimakiyar Firaminista Ukraine, Iryna Vereshchuk ta ce sun gaza kwashe fararan hula daga wadanan wurare da suka kasance masu hadari a yanzu, saboda Rasha taƙi mutunta tsasaita wuta.
Ta ce: “Mun shirya motoci dauke da kayayakin jin-kai, wanda ya kamata su isa Mariupol daga Zaporozhye. manyan motoci 8 da aka lodawa abinci da magunguna, da bas 30 domin taimakawa Mata da yara da tsoffi su fice daga Mariupol.
Duk wannan kokari bai yi aiki ba. Rasha ta ci gaba da luguden wuta har kan hanyar da motocin agajin za su ratsa. A yau Rasha ta hana mu kai dauki kokarin mu ya tashi a banza.”
Gwamnatin Ukraine dai ta tuntubi Poland domin samun damar amfani da jiragen yakinta don fuskantar Rasha.
Amurka ma ta ce tana kan tattaunawa domin maye gurbin jiragen Poland da wasu na daban idan an daidaita.
Nan da kwanaki kadan ake sa ran majalisar Amurka za ta amince da tallafin dala biliyan 10 ga al’ummar Ukraine. Za a kashe kudaden ne a fanin taimakon soji da ayyukan agaji.