Rasha; Takunkumin Da Kasashen Turai Suka Sanya Ba Zai Shafi Huldar Kasuwancinmu Da Iran Ba.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov a baya bayan nan yayi ikirarin cewa takunkumin da kasashen turai suka kakabawa kasarsa ba zai shafi alakar kasuwanci dake tsakaninta da kasar Iran ba,
A taron manema labarai da yake yi da a duk mako kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Saed Khatib zade da yake amsa tamabyar da aka yi masa kan bayanan da kasar rasha tayi kan alakarta da iran ya fadi cewa anasu bangaren suna ci gaba da bibiyar tattaunawar da ake yi a Vieanna kuma kasar Rasha tana taka muhimmiyar rawa na ganin an cimma yarjejeniya
Ya ce muna saurarin martani na diplomasiya game da wadannan kalaman kuma akwai bukatar Karin haske game da batun, tawagar iran a tattaunawar Vieanna suna nema abin da zai amfani Alummar Iran ne,kuma ana daukar matakai na cimma wannan burin,
Da yake bayani game da tattaunawa kai tsaye tsakanin iran da Amurka ya ce matsayin iran kan wannan batun abu daya ne kuma ba zai canza akan shi ba, muna yanke shawara ne bisa dabi’ar Amurka , a fili yake cewa Amurka ta fice daga cikin Yarjejeniya hadin giuwa ta JCPOA kuma babu ma wani canji a halayen Amurka ba a aikace.