Isra’ila ta tattara wasu manya-manyan bututai da za su malala ruwa cikin gine-ginen karkashin kasa da kungiyar Hamas take amfani da su a Gaza da aka mamaye a yunkurin fatattakarsu daga ciki, kamar yadda jaridarWall Street Journal ( WSJ) ta Amurka ta rawaito, inda ta ambato wasu jami’an gwamnatin kasar.
A tsakiyar watan Nuwamba, rundunar sojin Isra’ila ta gama kafa manyan bututai akalla biyar a wani wuri mai nisan kusan mil daya daga arewacin sansanin ‘yan gudun hijira na Al Shati wadanda za su iya sheka ruwa da yawansa zai kai dubban kyubik mita cikin awa daya, domin mamaye dukkan gine-ginen karkashin kasar cikin makonni kadan, in ji rahoton.
Babu cikakken bayani kan ko Isra’ila za ta malala ruwan kafin a saki dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, a cewar labarin. A baya Hamas ta ce ta ajiye dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su a “wurare masu aminci da kuma gine-ginen karkashin kasa.”
A lokacin da aka yi masa tambaya game da wannan batu, wani jami’in gwamnatin Amurka ya ce yana da kyau Isra’ila ta lalata gine-ginen karkashin kasar kuma kasar tana duba hanyoyi daban-daban na yin hakan.
Jaridar Wall Street Journal ta ce wani jami’in Rundunar Tsaron Isra’ila ta Defense Forces [IDF] ya ki cewa uffan kan wannan shiri ko da yake ta ambato shi yana cewa: “Rundunar IDF tana yin aiki domin kawar da ta’addancin Hamas ta hanyoyi daban-daban, inda take amfani da karfin soji da kuma fasahohi.”
0123 GMT — Kungiyar bayar da agaji ta Palestine Red Crescent ta daina jin duriyar ma’aikatanta da ke Gaza
Kungiyar bayar da agaji ta Palestine Red Crescent Society ta ce ta daina jin duriyar tawagar likitocinta da ke yankin Gaza da aka mamaye.
Ta bayyana haka ne bayan kamfanin sadarwa na Palestine Telecommunications Company [PalTel] ya ce an katse dukkan sadarwa da intanet a Gaza.
“Mun daina jin duriyar ma’aikatanmu da ke Zirin Gaza sakamakon matakin da Isra’ila ta dauka na katse dukkan kamfanonin sadarwa,” in ji wata sanarwa da Red Crescent ta fitar.
Ta bayyana matukar damuwarta game da rashin tsaron da tawagarta ke ciki a Gaza sakamakon luguden wutar da jiragen yakin Isra’ila suke yi a yankin.
Kungiyar ta ce katse hanyoyin sadarwar zai shafi masu kai agajin gaggawa a wuraren da aka yi wa luguden wuta a Gaza da kuma zai hana mutanen da ke neman agajin gaggawa kiran layin waya na gaggawa mai lamba 101 domin nean dauki.
0109 GMT — Dakarun Isra’ila sun kashe Falasdinawa 2 a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan
Dakarun Isra’ila sun kashe Falasdinawa biyu a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
Anas al Farroukh, mai shekara 23, da Mohammad al Farroukh, mai shekara 22, dukkansu sun samu munanan raunuka kafin a bayyana cewa sun mutu a asibiti, kamar yadda wani jami’i ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA, yana mai ambato Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu.
WAFA ya kara da cewa lamarin ya faru ne a yankin Ras Al Aroud a garin Sa’ir a arewa maso yammacin Hebron.
Source: TRTHAUSA