Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce matsalar kiba fiye da kima da ta zama tamkar annobar tana haddasa mutuwar sama da mutane miliyan 1 da dubu dari 2 duk shekara, tana mai kira da a gaggauta sauye sauye ga manufofi don dakile wannan al’amari mai hadari.
Hukumar lafiyar ta duniya (WHO) ta ce fiye da rabin baligai a nahiyar Turai na fama da wannan matsalata teba, sama da kowace nahiya idana aka debe yankunan Latin Amurka.
Ofishin hukumar lafiyar a nahiyar Turai ta ce kiba fiye da kima ta kai munzulin da za a bayyana ta a matsayin annoba a fadin nahiyar, kuma tana ci gaba da ta’azzara.
Alkalumman baya bayan nan da aka samu daga shekarar 2016 na nuni da cewa kashi 59 na baligai da kusan kowane yaro da cikin 3 na fama da lallurar kiba fiye da kima.
Masu binciken da suka saki wannan rahoto sun ce ba abubuwa da dama ne ke haddasa kiba fiye da kima da suka hada da amfani nau’ukan abincin da ba su dace ba da kuma rashin motsa jiki.
A wani labarin na daban Jami’an soji da wasu shaidun gani da ido sun ce mayakan kungiyar Al-Shabaab dauke da muggan makamai sun afkawa wani sansanin sojojin kungiyar tarayyar Afrika AU da ke Somalia a ranar Talata, inda aka yi kazamar arrangamar da ta yi sanadin salwantar rayuka a bangarorin biyu.
Bayanai sun ce, rundunar sojojin na AU ta aike da jirage masu saukar ungulu bayan farmakin da mayakan na Al Shebaab suka kaddamar kan sansanin sojojin wanzar da zaman lafiya da dauke da dakarun Burundi, wanda ke kusa da Ceel Baraf, wani kauye mai tazarar kilomita 160 daga arewa maso gabashin Mogadishu babban birnin Somalia.
Wani babban hafsan sojin Burundi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kimanin sojoji 30 ne suka mutu, wasu 22 kuma suka jikkata, yayin da wasu goma suka bace, said ai babu wani tabbaci game da adadin mutanen da aka kashe daga jami’an Somalia ko AU.
Kwamandan sojojin yankin Mohamed Ali ya shaida wa AFP ta wayar tarho cewa mayakan na Al Shebaab sun kaddamar da harin ne ta hanyar amfani da wata mota makare da bama-bamai, kafin daga bisani a fara musayar wuta tsakaninsu da dakarun na kungiyar AU.
Wannan dai shi ne hari na farko da aka kai kan sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na AU, tun bayan da aka sabunta rundunar wanzar da zaman lafiya ta AU a Somalia gami da sauya mata suna daga AMISOM zuwa ATMIS a ranar 1 ga watan Afrilu.
Majiyar sojan Burundi ta ce mayakan Al Shebaab kimanin 400 ne suka afkawa sansanin sojin na AU bayan da suka tarwatsa wasu bama-bamai da motoci guda biyu. Daga nan ne sojojin Burundin suka koma wani tsauni da ke kusa inda suka ci gaba da fafatawa, tare da samun tallafin jirage marasa matuka da jirage masu saukar ungulu.
A wata sanarwa da mayakan masu ikirarin Jihadi suka fitar, sun ce sun karbe iko da sansanin bayan kashe sojojin kungiyar Tarayyar Afirka 173, tare da fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna gawarwakin sojojin da aka kashe a kwance a kasa.
Ba a dai iya tantance adadin mutanen da suka mutu da bidiyon ba.