A rahoton da jaridar Arab Post ta bayar, ofishin Yair Lapid, firaministan gwamnatin yahudawan Sahayoniya, ya sanar a cikin wata sanarwa cewa, Isra’ila da Turkiyya sun yanke shawarar dawo da huldar jakadanci gaba daya da kuma musayar jakadu.
A cikin wannan bayani an bayyana cewa: Ci gaban dangantakar zai taimaka wajen zurfafa huldar da ke tsakanin bangarorin biyu, a bangaren tattalin arziki, kasuwanci da al’adu.
A wani bangare na bayanin ofishin firaministan gwamnatin yahudawan sahyoniya ya bayyana cewa: Bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin firaministan Isra’ila Yair Lapid da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Isra’ila da Turkiya sun yanke shawarar mayar da jakadunsu a ofisoshin jakadancinsu domin ci gaba da hulda.
Kamfanin dillancin labaran Anatoliya ya habarta cewa, a nasa tsokaci na farko kan sanarwar da Isra’ila ta yi na musayar jakadu da Ankara, ministan harkokin wajen Turkiya ya yi ikirarin cewa: “Za mu ci gaba da kare hakkin Falasdinu.”
Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Çavuşoğlu ya kuma bayyana cewa, Isra’ila da Turkiyya za su tura jakadu, wani muhimmin mataki a yunkurin da bangarorin biyu ke yi na daidaita alaka.
Shi ma shugaban gwamnatin yahudawan Isaac Herzog ya rubuta a shafinsa na Tuwita game da haka: inda ya ce; na yaba da sake dawo da cikakkiyar huldar jakadanci tsakanin Isra’ila da Turkiyya.
Wannan wani muhimmin ci gaba ne da muka jagoranta a cikin shekarar da ta gabata kuma zai taimaka wajen samar da karin dangantakar tattalin arziki, yawon bude ido da abokantaka tsakanin Isra’ila da Turkiyya.
Source: IQNA