Jam’iyyar Islama ta Ennahdha dake kasar Tunisia ta gargadi gwamnatin kasar da koda sunan wasa kada ta kuskura ta ce za ta cire sunan Islama a sabon kundin tsarin mulkin kasar da ake rubutawa yanzu haka, wanda ake sa ran gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a a kansa a wata mai zuwa.
Sabon kundin tsarin mulkin na daga cikin sauye sauyen da shugaban kasa Kais Saied ya saka a gaba, bayan ya kori majalisar dokoki da wasu manyan alkalan kasar.
ENNAHDHA ce babbar jam’iyya a majalisar tunisia da aka rusa kuma mai karfin fada aji kafin shugaba Saied ya karbi iko.
Jam’iyyar ta ja kunnen shugaban kasar da ya kauce wa kai hari a kan manufofin jama’ar kasar da suka hada da kabilarsu ta Larabawa da kuma addinin su na Islama.
Sadeq Belaid, lauyan da aka dora wa alhakin rubuta sabon kundin ya bayyana sabbin tanade tanaden da suke yi wanda ya kunshi share batun addinin Islama a cikin sabon kundin sabanin yadda yake a da, inda yake cewa ba za su amince da amfani da addini wajen siyasa ba.
A ranar 25 ga watan Yuli mai zuwa ake saran jama’ar kasar su kada kuri’ar amincewa da sabon kundin ko kuma watsi da shi.