Dubban al’ummar Tunisia sun gudanar da zanga-zangar adawa da matakin shugaba Kais Saied bayan matakinsa na baya-bayan da ke sake kara wa kansa karfin iko fiye da sashen shari’a lamarin da bangaren adawa ke kallo a matsayin kama karya.
Sa’o’i bayan sanar da wannan mataki a jiya lahadi, al’ummar Tunisia fiye da dubu 2 sun yi dandazo a tsakar birnin Tunis galibinsu riko da tutar kasar tare da rera wakokin kalubalantar abin da suka kira kama karyar shugaban.
Masu zanga zangar na Tunisia sun rabu gida biyu ta yadda wasu ke tambaya cikin wake wasu kuma na amsawa suma dai a cikin waken.
Rukunin farko na masu zanga-zangar cikin sigar tambaya na rera wakar cewa al’ummar Tunisia me kuke sai rukuni na biyu ya amsa da cewa kawo karshen kama karyar gwamnati, kwatankwacin juyin juya halin gwamnatin Zine El Abidine Ben Ali shekaru 10 da suka gabata, matakin da ke nuna cewa suna bukatar faduwar gwamnatin.
Wani rukuni daban na masu zanga-zangar na rera waken bukatar ceto demokradiyyar kasar.
Matakin na Kais Saeid na zuwa ne mako guda bayan shugaban na Tunisia ya sha alwashin rushe babbar majalisar shari’ar kasar wadda ya zarga da assasa zanga-zanga a kasar.
A wani labarin na daban kuma Dubban ‘yan Tunisia ne suka taru a kusa da majalisar dokokin kasar a yau Lahadi domin nuna adawa da kwace ikon mulkin shugaban kasa da suka kira juyin mulki.
Masu zanga-zangar sama da 3,000 ne suka taru, suna ta kururuwar cewa su na son a kawo karshen juyin mulkin da kuma aikin shugaba Kais da ke kokarin haifar da yakin basasa, tare da bayyana shugaban kasar a matsayin “wakilin mulkin mallaka.
Kamfanin dillancin labarai na Faransa, ya ruwaito cewa wasu daga cikin fusatattun masu zanga-zangar na dauke da alluna da ke nuna adawa da yiwa kafafen yada labarai barazana da kuma neman Hukumar shari’a mai zaman kanta.