Kungiyar Taliban tace kada Sojojin kasashen waje su yi ‘fatan’ ci gaba da kasancewa a Afghanistan bayan Amurka da NATO sun gama janye sojojinsu, tana mai gargadi danagene da tsaron ofisoshin jakadanci da filayen jiragen saman da ke zama alhakin dakarun Afghanistan.
Hakan na zuwa ne yayin da jami’an diflomasiyyar kasashen yamma da jami’an soji ke shirin tattaunawa kan yadda za a samar da tsaron ga duk wani farar hula da zai ci gaba da kasancewa a kasar nan gaba.
Sojin Turkiya
Rahotanni sun ce Turkiyya ta ce a shirye take ta ci gaba da kasancewa da dakarunta a Afghanistan domin kare filin jirgin saman Kabul, babbar hanyar fita ga jami’an diflomasiyyar kasashen yamma da ma’aikatan jin kai.
Fargaba
Kasar Amurka na cikin matakan karshe na kammala janye dakarunta da na NATO, kafin ranar 11 ga watan Satumba, dai-dai lokacin cika shekaru ashirin bayan da suka mamaye Afghanistan tare da kawar da Taliban.
Wannan na zuwa ne sakamakon fargaba da wasu kasashen duniya ke yi dangane da tsaron ma’aitakan kasashen su dake Aghanistan suna zaluntar bayin Allah bayan kammala ficewar dakarun Amurka da NATO a kasar Afghanistan, sakakon barazar komen Taliban.
A wani labarin na daban mai kama da wannan mayakan kungiyar Taliban sun hallaka wasu ma’aikatan kwance bama-baman kan hanya mutum 10 a yankin Baghlan na Afghanistan yau Laraba, wanda ke matsayin hari na baya-bayan nan da kungiyar ta’addancin ta kaddamar duk da kokarin kawo karshen yakin kasar na kusan shekaru 20.
Ma’aikatar cikin gida ta Afganistan da ke fitar da sanarwa kan harin, ta ce mayakn kungiyar ta Taliban sun shiga farfajiyar hukumar da ke aikin kwance bama-baman tare da yin kan mai uwa da wabi wajen harbe harbe da ya kai ga kisan jami’an 10.
Kakakin ma’aikatar Tareq Arian da takwaransa na gwamnan Baghlan sun shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne tun a yammacin jiya talata inda maharan suka kaddamar da farmakin da rufaffun fuskoki.
Afghanistan dai na jerin kasashe mafi yawan bama-bamai birne a karkashin kasa sakamakon tsawon shekarun da aka shafe ana gwabza yaki tsakanin kungiyoyin ta’addanci da Sojin gwamnati.
Hare-haren kungiyar ta Taliban da kisan fararen hula sun sake tsnanata a kasar ne tun daga ranar 1 ga watan Mayu lokacin da Sojin Amurka suka fara ficewa daga kasar.