Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa dan takarar shugabancin Faransa na jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi Eric Zemmour ya tsaya kan bakansa tare da jajircewa kan manufofinsa a yakin neman zaben da ya ke yi a sassan kasar.
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a game da hasashen zagayen farko na zaben na nuna cewa Zemmour ke da kashi 14 cikin dari na yawan kuri’un wato kankankan da Marine Le Pen ita ta jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi amma kuma kasa da Valerie Pecresse ta jam’iyyar ‘yan mazan jiya da ke da kashi 16 da rabi na yawan kuri’un dukkaninsu kasa da shugaba Emmanuel Macron mai kashi 24.
Sanarwar da tawagar yakin neman zaben Zemmour ta fitar bayan zantawar da Trump ta ce masu tsattsauran ra’ayin biyu sun tattauna kan batutuwa masu alaka da ‘yan cirani tsaro da kuma tattalin arziki dama alakar kasashen biyu a nan gaba.
Trump da Zemmour na da ra’ayi kusan iri guda ne la’akari da cewa kowa na da kyamar baki haka zalika na sanya manufofin kasarsa gaban komi.
Sanarwar ta ruwaito tsohon shugaban na Amurka wanda ya sha kaye hannun Joe Biden a zaben 2020 na shaidawa Zemmour cewa yana bukatar dagiya da jajircewa gabanin cika burinsa a kasar ta Faransa.